1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadakar kawo sauyi a Aljeriya

Yusuf Bala Nayaya
February 20, 2019

Wasu manyan jiga-jigai na siyasa a kasar Aljeriya sun tsara ganawa don fitar da wani dan takara na hadaka da zai kalubalanci Shugaba Abdelaziz Bouteflika a zaben da za a yi ranar 18 ga watan Afrilu.

Algerien Proteste Bouteflika
Hoto: picture-alliance/dpa

Abdallah Djaballah shugaban jam'iyyar adawa ta Algeria's Justice and Development Front ta masu kishin addinin Islama shi ya yi wannan kira a wannan Laraba don samar da wani kadami na tunkarar gwamnati mai ci.

Tsohon shugaban gwamnati Ali Benflis da Ahmed Benbitour da ma mai matsakaicin kishin addinin Islama Abderrazak Makri, na daga cikin wadanda suka nuna sha'awarsu ta shiga wannan hadaka da kananan jam'iyyu.

Wasu dai daga cikin jam'iyyun siyasa a kasar ta Aljeriya sun bayyana cewa za su kaurace wa zaben na watan Afrilu wanda a cewarsu an tsara shi don ya ba da dama ga ci gaba da kasancewar Bouteflika a kan karagar mulkin da yake tun a shekarun 1990.