Mutum 6 sun mutu a hadarin jirgin sama
December 9, 2018Talla
A sanarwar da mahukuntan Sudan suka fitar bayan aukuwar lamarin , sun ce akwai gwamna guda da kuma ministan ma'aikatar noma daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a hadarin. Wasu shedun gani da ido sun ce jirgin ya kama da wuta bayan da ya daki wani karfe inda daga bisani ya fado kasa. Lamarin ya auku a wani yanki da ke a gabashin kasar.