1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadarin jirgin ruwa ya kashe mutane a Afirka ta Yamma

August 31, 2025

Wani hadarin jirgin ruwa ya yi sanadin salwantar rayukan gomman wasu 'yan asalin nahiyar Afirka masu kokarin tsallakawa zuwa kasashen waje. Hukumomi a Gambiya ne suka tabbatar da faruwar lamarin.

Bakin haure 'yan Afirka masu neman tsallakawa ketare
Bakin haure 'yan Afirka masu neman tsallakawa ketareHoto: picture-alliance/AP/Libyan Coast Guard

Akalla mutane 70 ne suka rasa rayukansu a lokacin da wani jirgin ruwa dauke da ‘yan gudun hijira ya kife a gabar tekun Yammacin Afirka, in ji ma'aikatar harkokin wajen Gambiya a ranar Juma'a da daddare.

Wannan na daga cikin manyan hadurran da suka fi muni a ‘yan shekarun baya-bayan nan a kan hanyar hijira zuwa Turai.

A cewar sanarwar ma'aikatar, ana fargabar wasu mutane 30 sun mutu bayan jirgin wanda ake kyautata zaton ya tashi daga Gambiya dauke da mafi yawancin ‘yan asalin Gambiya da Senegal ya nitse a gabar tekun Mauritaniya da safiyar ranar Laraba.

Jirgin ya taso dauke da kusan fasinjoji 150, inda aka ceto mutum 16 kacal. Hukumomin Mauritaniya sun gano gawarwaki 70 a ranakun Laraba da Alhamis, kuma bayanai na nuna yiwuwar mutuwar fiye da mutum 100.