Hadarin jirgin sama a kasar Sudan
August 19, 2012
Talla
Rahotani daga Khartum babban birnin Sudan sun tabbatar da aukuwar hadarin wani jirgin saman kasar inda a ka bada sanarwar mutuwar a kalla mutane 31 ciki har da Abdel Hafiz Abdoul-Rahim ministan yawon bude idanun kasar da shi da wata tawagar jami'ai da ke kan hanyar su ta zuwa kudancin Kardofan gurin shugulgullan sallar 'Aidr Fitir ta karshen watan ramadan.
A yau da sanhin safiya ne gidan talbijan malakar gwamnatin kassar ta bada sanarwar wannan hadarin wanda kawo yanzu hukumomin kasar basu fayace musabbabinsa ba.
Mawallafa: Issoufou Mamane
Edita: Usman Shehu Usman