1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadarin jirgin sama a kurmin Amazon na kasar Brazil

September 30, 2006
Rundunar sojin saman kasar Brazil ta kaddamar da wani bincike don gano wani jirgin saman fasinja da ya bace a cikin kungurmin dajin Amazon. Hukumomin kula da zirga zirgar jiragen sama na Brazil sun ce jirgin na kamfanin Gol Airlines na dauke da mutane kimanin 150 lokacin da bace daga alllon masu kula da tashi da sukar jirgin sama. Jirgin na kan hanyar sa ne daga birnin Manaus na jihar ta Amazon zuwa Brasilia babban birnin kasar. A kuma halin da ake ciki kafofin yada labarun kasar sun rawaito cewa jirgin saman ya fadi cikin wata gona bayan ya yi karo da wani karamin jirgin sama na wasu mutane. To amma karamin jirgin saman ya sauka lafiya.