Hadarin jirgin saman Kenya ya halaka dukkan mutanen cikinsa
October 28, 2025
Hadarin jirgin saman kasar Kenya mai suna Mombasa Air Safari, ya yi sanadiyyar mutuwar dukkan fasinjoji 11 da ke cikinsa, wadanda Jamusawa ne da 'yan kasar Hungary, kamar yadda kamfanin jirgin ya sanar a wannan Talata.
Shugaban kamfanin John Cleave, ya ce fasinjoji 8 ne 'yan kasar Hungary sai Jamusawa 2, da kuma direban jirgin 'dan kasar Kenya.
Karin bayani:Kariyar hadduran jirajen sama a Afirka
Jirgin ya taso ne da asubahin wannan rana ta Talata daga yankin Diani na kasar da ke zama matattarar shakatawar 'yan yawon bude ido, a kan hanyarsa ta zuwa wurin shakatawa na Maasai Mara National Park da ke yankin Kichwa Tembo.
Tuni hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Kenya ta kaddamar da binciken musabbabin faruwar hadarin.
Ko a cikin watan Agustan 2025 makamancin hadarin ya halaka mutane 6, tare da jikkata wasu 2 a Nairobi babban birnin kasar.