1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ce ta harbo jirgin saman Ukraine

Abdul-raheem Hassan LMJ
January 11, 2020

Babban kwamandan sojojin saman juyin-juya halin kasar Iran, ya ce sun dauki alhakin kakkabo jirgin Ukraine bisa kuskure, sai dai hakan ya faru ne kan matsalar sadarwa da aka samu.

Iran 2019 | General Amir Ali Hajizadeh, Revolutionsgarden
Babban kwamandan sojojin saman Iran Amir Ali HajizadehHoto: Getty Images/AFP/A. Kenare

Babban kwamandan sojojin sama na kasar ta Iran Amir Ali Hajizadeh ya ce a lokacin da dakarunsa suka seta jirgin suna masu dakon harin martani ne daga Amirka ne.

A cewar kwamandan sojojin, lokacin da jirgin Ukraine ke kokarin keta hazon Iran kusa da sansanin sojoji da ke Tehran, an yi kokarin tuntubar kwararru dan shawara amma haka ba ta cimma ruwa ba. Sai dai duk da haka, Hajizadeh ya ce ya dauki baki dayan alhakin kuskuren da aka tafka wajen kai harin da ya yi sandiyyar faduwar jirgin tare da halaka baki dayan mutane 176 da ke cikinsa, mafi yawansu 'yan kasar ta Iran. A wani jawabi da ya yi ga manema labarai, ya bayyanaa cewa da ma ya mutu maimakon fasinjojin.

Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Noroozi

Shugaba Hassan Rouhani da na Ukraine Volodymyr Zelensky sun tattauna ta wayar tarho, inda Rouhani ya sha alwashin sake zurfafa bincike kan harin. Wannan na zuwa ne bayan da Shugaba Rouhanin ya amince da kuskuren sojojinsa tare da mika jeje ga Ukraine da sauran wadanda abin ya shafa.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yabawa kasar Iran game da yadda mahukuntanta suka dauki alhakin musabbabinn rikitowar jirgin saman kasar Ukraine mai dauke da fasinjoji 176. Merkel ta yi wannan tsokaci ne yayin ganawar ta da shugaba Vladmir Putin na kasar Rasha a birnin Moscow a wannan rana ta Asabar. Tun da farko Iran ta bayyana juyayi da alhinin afkuwar al'amrin wanda ya faru bisa kuskure tare da jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a cikin jirgin. 

Yanzu haka dai shugabannin biyu sun bukaci Iran da sauran kasashen da hadarin ya rutsa da al'ummarsu, da su gaggauta lalubo mafita. A nasa bangaren, shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya bukaci Iran da ta gaggauta hukunta wadanda ke da alhakin kakkabo jirgin saman fasinjan. Shi ma jagoran addinin kana babban jagoran juyin-juya halin Musulumci na Iran din, Ayatollah Ali Khamenei bayan da ya mika sakon jaje da ta'aziyya ga iyalan mamatan, ya bukaci rundunar sojojin kasar da ta gudanar da bincike kan lamarin.