1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hadarin mota ya halaka mutane sama da 20 a Cote d'Ivore

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 11, 2024

Kasar ta fara binciken musabbabin faruwar hadarin, sannan ta gargadi masu ababen hawa da su rinka kiyaye dokokin tuki.

Kenia Tote bei schwerem Autounfall
Hoto: AP/dpa/picture alliance

Hukomomin kasar Cote d'Ivore sun tabbatar da mutuwar mutane 21 tare da jikkatar wasu 10, sanadiyyar hadarin mota da ya ritsa da su cikin daren Lahadi.

Sanarwar da ma'aikatar sufurin kasar ta fitar a Litinin din nan ta ce tuni ta kaddamar da binciken musabbabin faruwar hadarin, sannan ta gargadi masu ababen hawa da sun rinka kiyaye dokoki da ka'idojin kan hanya, don kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

Karin bayani:Shugaba Ouattrara ya tsige firaministansa

Ko a farkon shekarar nan wata tankar dakon mai ta banke motar bas mai dauke da fasinjojin a arewacin kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13, wasu 44 kuma suka samu raunuka.