1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hadarin mota ya hallaka bakin haure 'yan Afirka a Mexico

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 5, 2024

Hukumar kula da shige-da-ficen kasar bata kai ga sanar da musabbabin hadarin ba, wanda ya faru a kusa da iyakarta da Amurka

Mexiko Tepic | Bus-Unfall
Hoto: ULISES RUIZ/AFP

Wani hadarin mota a kudancin kasar Mexico ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan ci-rani 3, biyu daga cikinsu 'yan asalin kasar Kamaru, yayin da wasu 5 kuma suka jikkata.

Karin bayani:Mexico ta ayyana dakile kwararar bakin haure

Hukumar kula da shige-da-ficen kasar bata kai ga sanar da musabbabin hadarin ba, wanda ya faru a kusa da iyakarta da Amurka, wadda ta yi kaurin suna wajen samun bakin haure masu kokarin tsallakawa cikin Amurka.

Karin bayani:Mexico: Hatsarin mota ya kashe bakin haure 53

Ko a bara wasu baki haure 16 sun mutu sakamakon hadarin mota a kan wannan hanya, wadanda 'yan asalin kasashen Venezuela ne da da Haiti.