Hadarin mota ya kashe masu bikin addini a Senegal
August 17, 2025
Hadarin mota ya yi ajalin masu ziyarar ibada 33 akasar Senegal, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Touba, guda daga cikin birane masu tsarki ga mabiya darikar Tijjaniya.
Ma'aikatar agajin gaggawa ta kasar ta sanar da cewa bayan wadanda suka mutun, akwai wasu da dama a karkashin kulawar likita, bisa hadurra dabam-daban da aka samu na ababen hawa a bikin addinin mafi girma a kasar Senegal
Senegal ta haramta amfani da babura a kan iyakokinta da Mali
Dubun dubatar mabiya darika na dafifi a birnin Touba domin ibadar shekara-shekara da ake kira Magal, wace ta samu asali daga wani fitaccen malamin addinin yankin Cheikh Ahmadou Bamba tun a shekarar 1895.
Mabiyan kan fito daga ko ina cikin Senegal, da kasashen yammacin Afirka ciki har da Nijar da Najeriya