1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar:Taron hafsoshin sojan ECOWAS a Ghana

August 17, 2023

Hafsoshi sojan kasashen kungiyar ECOWAS ko CEDEAO suna gudanar da babban taro a Ghana kan juyin mulkin Nijar.

Hoto: KOLA SULAIMON/AFP

Manyan hafsoshi sojan kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ko kuma CEDEAO sun bude babban taro a birnin Accra na kasar Ghana domin lalubo hanyoyin bullo wa sojojin Nijar wadanda suka hambarar da gwamnatin Mohammed Bazoum.

A yayin da yake jawabi babban hafsan sojin Najeriya, janar Christopher Musa ya ce ''burinsu ba kawai fito da dabarun tunkarar sojin Nijar ba ne, su na son samar da hanyoyin zaman lafiya mai dorewa a kasashen yankin yammacin Afrika baki daya''.

To sai gabanin taron ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta ce a shirye take da ta karfafa wa duk wani shiri na kasashen Afrika guiwa domin daidaita lamura a Nijar. Sannan kuma Jamus din ta bukaci kungiyar Tarayyar Turai da ta kakaba takunkumi a kan mambobin majalisar CNSP wadda ta kifar da gwamnatin farar hula a Nijar kuma ke ci gaba da watsi da duk wasu kiraye-kiraye na dawo da shugaban da suka hambarar kan kujerarsa.