1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Haile Selassie - ‘Zakin Judah na Habasha'

Yusuf Bala Nayaya LMJ
April 10, 2018

Sarkin babbar daula Haile Selassie, zakin Judah wanda ya gaji sarauta mai tsawon tarihi na shekaru aru-aru. Ya samar da sauyi na ci-gaba sabanin tunaninsa. Sauyin ya zama silar raba shi da gadon sarautarsa.

Bildergalerie Iran Historischer König Schah Mohammed Reza
Hoto: picture-alliance/Bildarchiv

Wane lokaci Haile Selassie ya rayu? 

Haile Selassie an haifeshi a ranar 23 ga watan Yuli na shekara ta 1892 a kusa da Harar cikin kasar Habasha, inda aka rada masa suna da Tafari Makonnen. Mahaifinsa tabbashi ne kuma na kusa da Sarki Menelik na II. An kira shi zuwa kotu a Addis Ababa lokacin da babansa ya mutu a 1906.

A 1916 ya zama mabiyin akidar Ras Tafari, da ake zaton ya gaji sarauniya Zauditu da ke zaman 'ya ga Menelik na II. A shekara ta 1928 tare da magoya bayansa sun sanya sarauniyar ta bashi sarauta.

A shekara ta 1930, bayan mutuwar sarauniya Zauditu an nada Tafari a matsayin sarki. An rinka kiransa Haile Selassie – "Babban mai aika sako". An masa juyin mulki karkashin jagorancin sojoji masu goyon bayan tsarin Kwaminisanci a shekara ta 1974, ya kuma rasu a ranar 26 ga watan Agusta na shekara ta 1975 a birnin Addis Ababa.

Ginshikan da Haile Selassie ya kafa: 

Ya gabatar da kundin tsarin mulki na farko a Habasha a shekarar 1931, wanda ke tafiya da tsarin majalisa da bangaren doka, ya kuma nuna cewa dukkannin al'ummar kasar ta Habasha daya suke. Sai dai kundin tsarin mulkin kasar na farko da wanda aka yi a shekarar 1955 sun sha suka bisa zargin ba da karfin iko ga sarkin kasar kasancewar yana da karfin iko da zai iya fatali da duk wani kudiri da majalisa ta cimma, sannan babu hurumi na kafa jam'iyyun siyasa.

Haile Selassie - ‘Zakin Judah na Habasha'

01:50

This browser does not support the video element.

Shin Haile Selassie ya fi karfin a soke shi?

Da fari dai Tafari Makonnen an kalle shi a matsayin mai tsare-tsare managarta, ana ganin yana da hannu wajen sauke Sarki Lij Ilyasu da Zauditu ta gada, wanda ya yi mulkin shekaru uku kacal. A matsayinsa na sarki mai iko Haile Selassie ya tura dalibai da dama zuwa kasashen waje domin karatu, daga baya wadannan dalibai su suka yi sanadin sauke shi daga mulki saboda kukan da suke na rashin samar da sauye-sauye. An yi yunkuri na yi masa juyin mulki a 1960, babbar barazana ga mulkinsa wanda daga karshe sojoji masu goyon bayan tsarin kwaminisanci suka yi gaba da kujerarsa.

Ta yaya Haile Selassie ya samu damar jan hankalin duniya?

A matsayinsa na wanda yake jerin wadanda za su iya sarauta, Tafari ya sanya Habasha a Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta 1923, daya daga cikin kasashen Afirka kalilan da ke cin gashin kansu, a lokacin kasarsa ce kadai ta samu damar zama mamba.

A 1963 sarkin ya bijiro da taron farko na kungiyar Hadin kan Kasashen Afirka (OAU) wacce daga bisani ta zama kungiyar Tarayyar Afirka (AU). Ya taimaka wajen fara tsara aiyukanta kana ya zamo shugabanta na farko, inda aka kafa helkwatarta a birnin Addis Ababa.

Ya Haile Selassie ke kallon Jamus?  

Ganin yadda yake neman hadin kan kasa da kasa ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashe dabam-dabam, a shekarar 1954 ya kasance shugaban wata kasar waje da ya fara ziyarar sabuwar gwamnatin Tarayyar Jamus, abin da ya sa ya samu gagarumar tarba da biki mai kayatarwa da ake wa duk wani babban bako da ya ziyarci Jamus tun bayan yakin duniya. Ya kasance a gaba wajen nuna sha'awarsa a fannoni na lafiya da aikin gona da masana'antu, wadanda ya yi burin gani a Habasha. Kasarsa ta zama kawa ga Jamus sannan Haile Salassie ya samu tarbar karramawa a birnin Bonn na Jamus, shekara guda kafin a kifar da gwamnatinsa.

Mene ne Haile Selassie ke fadi?

"Baya ga daular ubangiji, a wannan duniya, babu wata kasa da tafi wata,,,,,,,,,yau mu ne gobe kuma ku ne."

     -Jawabinsa ga taron Majalisar Dinkin Duniya a wancan lokaci a shekara ta 1936, ya yi kira da a kawo wa kasarsa dauki wajen fitar da dakarun Italiya masu mamaya.

"Tarihi ya koya mana cewa akwai karfi a hada kai, takatsantsan da dunkulewa waje guda da manta bambanci da ke tsakaninmu, zai taimaka gaya wajen ganin mun cimma burin da muka sa gaba, burin dai shi ne kasashen Afirka abokan juna masu hada kai."

      -Jawabin karbar jagoranci a kungiyar hada kan Afirka a 1963.

Me Haile Selassie ya barwa Habasha? 

Haile Selassie ya kafa mata jami'a ta farko da makarantu da asibitoci da gwamnati da ta tsaya da kafarta. Sauyin da ya kafa da ke da buri na bude kofar Habasha da sauran sassa na duniya. Al'ummomin kasa da kasa na yi wa sarkin kallon shugaba mai hikima, ana kuma girmama shi. Matsayin da ya zama mai amfani ga Afirka. Shugabannin Afirka na ganinsa a matsayin gwarzon da ya jagoranci kishi da ci-gaban Afirka. Bayan samun 'yancin kai shugabannin Turai na kallonsa a matsayin mai yaki da mamaya yayin da a Jamaica ake kallonsa a matsayin mai aika sako da wasunsu ke bautawa a matsayin mai ceto.

 

Wadanda suka yi hidima wajen hada labarin Jackie Wilson da Yilma Haile Michael karkashin shiri na musamman da DW kan tsara na Tushen Afirka bisa tallafi na gidauniyar Gerda Henkel.