1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar daukin rundunar tsaro zuwa Haiti

Abdoulaye Mamane Amadou
July 10, 2021

Kwanaki bayan kisan Shugaban Haiti Jovenel Moïse, hukumomi a kasar na fargabar ko birbishin kwamandojin da suka yi kisan ka iya kara dagula al'amura.

Haiti | Joseph Lambert
Hoto: HECTOR RETAMAL/AFP/Getty Images

Da yake zantawa da manema labarai babban jami'i a ma'aikatar zaben Haiti Mathias Pierre, ya ce kasar na da bukatar daukin dakarun gaggawa daga Amirka da Majalisar Dinkin Duniya domin kare filin jirgin sama da gabar teku hakan da hanyoyin safarar man fetur dinta, kana kuma tuni Amirka ta ce za ta tura wata tawagar 'yan sandan bincike ta FBI.

Ya zuwa yanzu dai mutane 28 ne aka kama galibi 'yan Kolombiya da ake zargin sun yi kisan gillar, ciki har da wasu 'yan Amirka biyu masu asali da Haiti, a yayin ga hukumomi a Kolombiyar suka tabbatar zargin wasu tsoffin soja 17 da hannu dumu-dumu wajan aikata laifin.

Sai dai duk wannan na zuwa ne a yayin da a share daya kasar ke neman fadawa cikin wani rudani na siyasa, inda firaministocin kasar wanda aka nada kwana daya a gabaninin kisan shugaban da mai barin gado ke bayyana kansu a matsayin shuwagabannin wucin gadi.