1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Safarar 'yan mata daga Najeriya zuwa Turai don yin karuwanci

Muhammad Bello AMA
July 30, 2019

Hukumomi a Jahar Edo da ke kudancin Najeriya sun kafa hukumar yaki da safarar 'yan mata don kai su kasashen Turai yin sana'anar karuwanci duba da yadda jihar ta yiwa sassan Najeriya shu'ura.

Nigeria Lagos International Polo Tournament 2019
Yan mata na kwalliyaHoto: Reuters/A. Sotunde

Safarar 'yan mata zuwa kasashen na Turai ta barauniyar hanya ci gaba da samun gindin zama a Najeriya duk da munanan hadduran da ke tattare da sana'ar da ta shafi salwantar rayuwa da fuskantar ukuba a hannun dilallan 'yan matan, baya ga kamuwa da cututtuka dabam-dabam 

Wannan matsalar mai tattare da daukar hankali ta sa hukumomi a jihar Edo suka kafa wata hukuma da ke yaki da safarar ta mutane musamman 'yan mata tare da mika jan ragamarta a hannun kwamishiniyar shari'ar jihar wacce a hira da DW Hausa, shugabar hukumar ta ce sun samu nasarori da dama ciki har da na wayar da kan 'yan mata da su rungumi sana'o'in hannu don dogaro da kai maimakon sana'anar ta karuwanci a Turai.

Samun makudan kudi a karuwancin 'yan matan Najeriya a Turai

Wasu 'yan mata da aka mayar daga LibiyaHoto: DW/K. Gänsler

Peace Daniel wata matashiya a Benin ta dora dalilin da yawan mata, da kuma kwawar neman mallakar manya-manayan gidaje da motoci masu kyau, wanda sau tari 'yan uwansu da suka samu damar tsallakawa zuwa Turai suka samu damar mallakar. 

Ita kuwa Madam Adesuwa da ta shafe tsawon shekaru 10 tana dilallancin 'yan matan zuwa ketare cewa ta yi "Ina da mutane a ko ina cikin wannan harka  kamar a Italiya,da Spain da Jamus. Daga Najeriya muna bi ne ta yankin sahara muna matukar wahala kafin cimma nasara, wasu 'yan matan kuma ba sa sanar da iyayensu inda za su tafi ba ni kuma idan suka mutu sai in share batun ba tare da na sanar da inda suka shiga ba. Ana samun riba domin a shekara daya ana samun miliyan biyu na dalar Amirka.

Rayukan dubban 'yan matan jihar Edo sun salwanta a anniyarsu ta zuwa Turai don sana'ar karuwanci haka kuma da dama daga cikinsu da suka dawo a gida sun dawo da cututuka ciki musamman ma cutar AIDS/SIDA.