1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a kasar Somaliya

April 21, 2004

Har yau kasar Somaliya na fama da hali na zaman dardar kuma ta rarrabu gida uku zuwa yankin kudanci tare da tsofuwar fadar mulki ta Mogadishu da yankin Puntland mai ikon cin gashin kansa sai kuma yankin Somali-Land mai ikirarin ballewa daga Somaliyar baki daya

Filin cin kasuwa a Mogadishun Somaliya
Filin cin kasuwa a Mogadishun SomaliyaHoto: AP

Kwararrun masana al’amuran tsaro na kasa da kasa na tattare da imanin cewar tuni yankin gabacin Afurka ya zama wani dandalin da ‚yan ta’adda ke neman mafaka a cikinsa kuma rusasshiyar kasar Somaliya ce akan gaba. Akwai kuwa muhimman dalilai game da haka. Domin kuwa ita Somaliya daya ce daga cikin kasashen da suka wargaje, ba su da wata gwamnati ta tsakiya dake da ikon hada kan al’ummarsu. To sai dai kuma duk da haka al’umar Somaliya sun dogara ne akan ayyukan noma da kiwon dabbobi. Kimanin kashi 70% na al’umar kasar suka dogara kacokam akan ayyukan noma. Kowane daga cikinsu kuwa yana tinkafo ne da kabilarsa kuma shuagabannin kabilun ne ke da fada a ji tun bayan wargajewar wannan kasa ta gabacin Afurka. Wadannan shuagabannin kabilu na da dakarun mayaka dake tsaron lafiyar jama’arsu. To sai dai kuma al’um,ar Somaliya ba mutane ne dake son tashe-tashen hankula ba, bisa sabanin yadda akan yi ikirari a hotunan da akan nunar ta gidajen telebijin a cewar Abdurrahaman Alan, wanda yayi shekara da shekaru yana kula da al’amuran ofishin jakadancin kasar a nan birnin Bonn. Ya kara da cewar:

Ikirarin da ake yi na cewar kowane dan kasar Somaliya yana da damarar makamai kage ne kawai. In har suna mallakar makamai to a yankuna ne da mutane ke tsoron farmaki daga ‚yan fashi. A yankuna da dama zaka tarar da kowa ya san kowa. A saboda haka, galibi ba a kauyuka ne ake samun mutane cikin damarar makamai ba, sai dai watakila a wuraren cin kasuwa inda mutane ke tsoron hari daga ‚yan fashi da makami.

Ko da yake ba a ba da la’akari sosa ga halin da take ciki, amma kasar Somaliya ta samu sararawa iya gwargwado. Kasar na da muhimmiyar tashar jiragen ruwa da kuma wani kasaitaccen filin saukar jiragen sama da aka gina tare da taimakon tsofuwar Tarayyar Soviet. A wadannan yankuna ba a fuskantar rikici saboda babu wata gwagwarmaya ta neman kama madafun iko tsakanin kabilu ‚yan kalilan dake akwai. A yankin kudancin Somaliya mai tsofuwar fadar mulki ta Mogadishu ne kawai ake ci gaba da fama da yakin basasa. Kuma kasashe makobta kamarsu Habasha da Kenya da kuma Jibuti sune ke rura wutar rikicin saboda basa kaunar ganin kasar Somaliya ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wadannan kasashe suna cin kazamar riba daga hali na zaman dardar da Somaliya ke ciki saboda cinikin makamai. Kowace daga cikin kasashen na bakin kokarinta wajen tabbatar da angizonta a Somaliyar ta kan shuagabannin kabilun da ba sa ga maciji da juna. Daya matsalar dake addabar Somaliya kuma ita ce ta aiwatar da ganyen Qat mai sa maye, wanda ya yadu tsakanin al’umarta, musamman ma maza. Da yawa daga abubuwa masu sa mayen akan shigo dasu ne daga kasashe makobta kuma ta haka suke kara kassara tattalin arzikin kasar ta Somaliya.