Halin da ake ciki a Kenya
January 2, 2008Rahotanni daga Kenya sun ce ɓangarorin biyu suna ci gaba da zargin juna da laifin kisan ƙare dangi,inda mai magana da yawun gwamnati Alfred Matua ya baiyana cewa ‘yan kabilar Luo ta Odinga suna ƙoƙarin kawadda ‘yan kabilar Kikuyu ta shugaba Kibaki yayinda mutane kusan 250 suka rasa rayukansu. Yana mai baiyana cewa ‘yan daba sun mamaye harkar siyasar.
A hannu guda kuma magoya bayan Odinga da mafi yawansu suka fito daga kabilar Luo sun zargi Kibaki da kisan kiyashi.Kabilar ta Kikuyu da Kibaki ya fito dai ta mamaye harkokin siyasa da kasuwanci na ƙasar Kenya da ta kasance mafi ci gaban tattalin arziki a gabacin Afrika.
A yau ɗin nan matasa sun fito ɗauke da adduna suna masu tare hanyoyi sa’oi kaɗan bayan an ƙona wasu ‘yan kabilar kikuyu cikin wani coci da suke ɓoye a lardin Eldoret.
Wani abu kuma da ya ƙara hura wutar tashe tashen hankulan shine kalaman da shugaban hukumar zaɓe Samuel Kivutu ya yi cewa, ba shi da tabbacin ko Kibaki ya ci wannan zaɓe.
Ƙasashen yammacin duniya dai a halin yanzu sunyi kira ga shugabannin siyasar Kenya da su sasanta tsakaninsu,sun kuma yi kira ga jama’ar ƙasashensu da su dakatar da zuwa yawon buɗe ido a ƙasar da ake ganin ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashe da suke da ingantacciyar demokradiya a Afrika.
A yau ɗin ne kuma ake sa ran shugaban Ƙungiyar Taraiyar Afrika John Kufour zai kai ziyara Kenyan a wani yunƙuri na shiga tsakani a rikicin.
Kasar Birtaniya wadda ta yi wa Kenyan mulkin mallaka ta yi kira ga ƙungiyar AU da ƙungiyar kasashe renon Ingila da su yi ƙoƙarin sasanta tsakanin Kibaki da Odinga waɗanda jam’iyunsu suka zargi juna da maguɗin zaɓe. Sai dai kuma kakakin gwamnati Alfred Matua yace ai ƙasar ba kudancin Sudan ba ne da za a nemi shiga tsakani
A dai ranar Lahadi ne aka rantsar da Kibaki bayan sakamakon zaɓen ya nuna cewa shi ya lashe zaɓen. Masu sa ido na Ƙungiyar Taraiyar Turai sunce zaɓen ya gaza cimma ka’idar ƙasa da ƙasa na demokradiya.
‘Yan sandan ƙasar sunce wannan rikici dai da ya ɓarke tsakanin kabilun biyu da suka daɗe suna zaman doya da manja yanzu haka ya tarwatsa jama’a fiye da 70,000.