1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a rikicin Libiya mai ban tsoro ne

March 9, 2011

Gadhafi ya zargi ƙasashen yammacin duniya da ƙoƙarin ƙwace arziƙin man fetur da Allah ya horewa ƙasarsa.

Moammar Gadhafi ya ki ya saduda ga bukatar sauka daga mulkiHoto: dapd

A yayin da dakarun dake biyayya ga shugaba Moammar Gadhafi ke ci gaba da jefa bama-bamai akan sansanonin 'yan tawayen ƙasar, ya kwatanta ƙasashen yammacin duniya da cewar 'yan mulkin mallaka ne kawai ke ƙoƙarin cin gajiyar arziƙin man fetur da Allah ya baiwa ƙasar, tare da wulaƙanta Libiyawa yadda za su kasance ba'yin su. Shugaban na Libiya, wanda ya gudanar da jawabin sa ta tashar telebijin na ƙasar a wannan Larabar, ya jaddada zargin da yake yiwa ƙungiyar Al-Qaeda laifin rikicin da ƙasar sa ta faɗa ciki tun a ranar 15 ga watan Fabrairun daya gabata. Ya shaidawa wata tashar telebijin ta ƙasar Turkiyya cewar - a faƙaice yana goyon bayan haramtawa jirage yin shawagi a Libiya domin a cewar sa a lokacin ne Libiyawa za su gane gaskiyar manufar ƙasashen yammacin duniya na ƙoƙarin ƙwace arziƙin man fetur nasu, kana su ɗauki makamai domin tinƙarar su.

Ci gaba da zubar da jini

Wannan bayani yana zuwa ne a dai dai lokacin da dakarun dake goyon bayan shugaba Gadhafi ke yin ruwan bama-bamai a garin Ras Lanuf mai arziƙin man fetur dake yankin gabashin ƙasar a wannan Larabar, wanda ya janyo turnuƙewar hayyaƙi kusa da cibiyar man fetur ta As-Sidra.

Hoto: dapd

A lokacin da ake ci gaba da gwabza faɗan ne kuma ministan kula a harkokin wajen ƙasar Italiya Franco Frattini ya sanar da cewar akwai wasu jami'an gwamnatin ƙasar Libiya da suka isa birnin Brussels domin ganawa da jami'an ƙungiyar tarayyar Turai da na ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO a ranakun Alhamis da kuma Jumma'a. A zaman da ƙungiyar ta EU ta yi ne kuma kantomar kula da manufofin ƙetare na ƙungiyar Catherin Ashton ta ce duk da cewar ƙofar tattaunawa a buɗe take, amma fa ba za su zura ido suna kallon lamura na ci gaba da taɓarɓarewa a ƙasar Libiya ba:

"Wasu lokutan tuntuɓar juna tafi amfani akan mayar da ƙasa saniyar ware. Akwai lokutan da ware ƙasa ke da ta'asiri, amma tuntuɓar juna tafi. Amma duk da wannan bayanin, ina ganin mu ne muka fitar da Gadhafi daga kotu a can baya, to yanzu kuma lokaci ya yi da zamu mayar da shi cikin kotun."

Gujewa ɗaukar matakin gaggawa

Duk da wannan furucin da jami'ar kula da harkokin ƙetaren ta yi dai, ministan kula da harkokin wajen Italiya Franco Frattini ya yi gargaɗin cewar kamata ya yi a bi lamarin Libiya sannu a hankali domin kaucewa tsunduma cikin wata babbar matsala bisa la'akari da abinda ya ce ziyarar da wani babban jami'in gwamnatin Libiya Manjo Janar Abdelrahman al-Zawi ya kai zuwa birnin alQahira na ƙasar Masar da kuma wata tawagar gwamnatin Libiyar dake birnin Brussels.

Kantomar kula da manufofin ƙetare na ƙungiyar EU Catherin AshtonHoto: dapd

Tun da farko a ganawar da kantomar kula da manufofin ƙetare na ƙungiyar tarayyar Turai Catherin Ashton ta yi da mai magana da yawun 'yan adawar Libiya Mahmoud Jebril gabannin zaman majalisar dokokin tarayyar Turai a birnin Srasbourg cewa yayi Libiyawa ba sa ƙaunar ganin sojojin ƙetare a ƙasar su:

"Za'a iya bin hanyoyi daban daban wajen tallafawa mutane a fafutukar kawar da Gadhafi. Haramtawa jirage yin shawagi ɗaya daga ciki ne, ga kuma samar musu da makamai. Sai dai Libiyawa suna Allah wadai da duk wani shiga tsakani na sojin ƙetare - kai tsaye. Kawai mun yi amannar cewar Libiyawa ne ya kamata su samarwa kansu makoma."

Ya zuwa yanzu dai ƙasashen duniya basu kai ga cimma matsaya guda ba dangane da yadda zasu warware rikicin ƙasar ta Libiya, wanda ke ci gaba da janyo mutuwar jama'a.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita: Ahmad Tijani Lawal