1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da 'yan Afirka baƙar fata ke ciki a sabuwar Libiya

September 2, 2011

Ƙasar Libiya wanda ta kasance mattarar baƙi daga ƙasashe matalauata musamman daga Afirka kudu da Sahara a zamanin gwamnatin Gaddafi, yanzu bayan kifar da gwamnatin Gaddafi, baƙaƙen fata na cikin wata uƙuba a ƙasar Libiya

Mustafa Abdel JalilHoto: picture alliance/dpa

A halin da ake ciki yanzu haka a ƙasar Libiya, baƙar fata na fuskantar kame-kame na ba gaira ba dalili. Ba tare da wata tabbatacciyar shaida ba, akan zarge su da laifin taimaka wa gwamnatin Gaddafi. A Benghazi ma dai rahotanni sun nuna cewar farautar baƙarfatar ake yi domin kisansu nan take, a yayinda a Tripoli suke fama da tsangwama iri-iri. Akasarin baƙar fatar dai tuni suka bar Tripoli tun bayan ɓarkewar rikicin, a yayinda waɗansunsu kuma, ga alamu, aka riƙa tilasta musu kama aikin sojan dole domin mara wa gwamnatin Gaddafi baya.....Wakilin DW Thibaut Cavailles ya hau da wasu daga cikinsu a Tripoli ya kuma aiko mana da wannan rahoton

A daidai lokacin da ya hango motarmu a wata unguwar da ake kira Taira a Tripolin Libiya, wani da ake kira Peter, nan take ya kutsa kai a cikinta. Bai kuma yi wata-wata ba wajen fara magana da mu, bayan da ya farga cewar mu 'yan jarida ne. Bayan da muka wuce wani shingen binciken da aka shata kan hanya, Peter daga Najeriya, dake cikin hali na ruu da rashin sanin tabbas ya kai mu mazauninsa, wanda wani an aramin aki ne dake da gadaje biyu da akwatin telebijin guda ɗaya. Sai kuma wasu 'yan ƙananan riguna dake ajiye a yashe. Peter na zama ne a wata unguwa mai cunkoson jama'a, ya kuma yi bayani yana mai cewar:

Yan tawayen Libiya suka kame baƙi a TiripoliHoto: dapd

Ya ce:"Lamarin na tattare da haɗarin gaske. Idan na fita kan hanya sai in riƙa waiwaye, dama da hagu, domin in tabbatar cewar ba mai bin sawuna. Ina da abokai masu tarin yawa, amma ban san inda suka shiga ba. Na sha kiransu ta salula amma layin na rufe."

Peter dai baƙar fata ne, wanda larabawa ke kiransa Abd, wato bawa. Ya je Libiya ne don neman aikin yi, daidai da sauran 'yan ci rani daga ƙasashe 'yan rabbana ka wadata mu, kamar Philippines da Masar da Bangladesh da makamantansu, waɗanda suke ayyukan da ainihin Libiyawa ke ƙyamar yinsu, kamar dai shara ko wanke motoci ko gadi a gidajen otel. Gwamnatin Gaddafi ta sha tuntuɓar wasu daga cikinsu ko zasu yarda su mara mata baya a gwagwarmayarta da 'yan tawaye, kamar yadda Peter ya nunar:

Ya ce:"Sun sha tambaya ta cewar: Ko zaka taimaka mana a wannan faɗa? Ni kuma a kodayaushe ni kan ce da su: a'a, ni kam ba na zo faɗa ba ne. Aiki ne ya kawo ni ƙasar nan domin kyautata makomar rayuwata."

'Yan tawayen Libiya ke murnaHoto: dapd

Akwai dai alamar gaskiya akan abin da Peter ke faɗa na cewar ba ya je Libiya ne don shiga rikici ba, duk da cewar akwai masu saka ayar tambaya a game da inda dukkan mayaƙan Gaddafi suka shiga.

Daga baya dai Peter ya kai mu gun wani ɗan Afirka mai gyaran gashi, wanda a zamanin baya baƙar fata kan taru a wurinsa, amma a yanzu kowa yayi ta kansa tun bayan da Tripoli ta faɗa hannun 'yan tawaye.

Wani da ake kira Steve daga Kamaru ya ƙara da jaddada cewar ko sau daya bai taɓa yi wa gwamnatin Gaddafi aiki ba tsawon rikicin Libiyan.

Amma tun bayan da 'yan tawaye suka kama birnin Tripoli misalin makonni biyu da suka wuce, baƙar fata suka shiga garari game da makomar rayuwarsu. Ba tare da wata tabbatacciyar shaida ba ake tuhumarsu da kasancewa sojan haya na Gaddafi, kamar dai Steve, wanda ya musunta dukkan zargin da ake masa.

Wannan dai wani ƙazafi ne mai tsananin gaske, wanda ba mu da ikon tabbatar da gaskiyarsa. Ƙungiyar neman afuwa ta Amnesty dai tuni ta kutsa Libiya domin bincike akan ire-iren wannan zargin da ake wa baƙar fatar Afirka 'yan ci-rani a Libiya, wanda bisa ga dukkannin alamu, ba kome ba ne illa wani mataki na ramuwa, kamar yadda aka ji daga wakiliyar Amnesty Samira Boussalama.

Mawallafi: Ahamadu Tijjani Lawal

Edita: Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani