1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tanzaniya ta karbi bakin haure dubu 355

Umar Zahradeen Abdul-raheem Hassan
June 20, 2018

Dubban 'yan kasashen Jumhuriyar Demokradiyyar Kwango da Burundi da ke samun mafaka a Tanzaniya, sun koka da kuncin rayuwa da suke fuskanta a sansanoninsu.

Ruanda UNHCR Flüchtlingslager Burundische Flüchtlinge
Hoto: picture-alliance/dpa/D. Kurokawa

A ranar tunawa da 'yan gudun hijira da Majalisar Dinkin Duniya ke yi a duk shekara, a bana ranar ta maida hankali kan duba halin da 'yan gudun hijiran ke ciki a duniya tare da nazarin magance matsalolin. Akalla 'yan gudun hijira dubu 355 ne ke zaune a sansanoni daban-daban a Tanzaniya wadanda suka fito daga Jumhuriyar Demokaradiyyar Kwango da Burundi sakamakon rikice-rikice. Ilakoze Abel dan gudun hijira ne da ya fito daga Burundi ya kuma ce "ina da damar yin abubuwa daban-daban domin in nemi na kaina sabanin a wanann sansanin 'yan gudun hijirar na Tanzaniya. Ba a barinmu mu fita waje mu yi aiki. Abincinmu da sauran bukatu sun dogara ne kan Majalisar Dinkin Duniya ke kawo mana."

'Yan gudun hijira na jiran magani a TanzaniyaHoto: Reuters/T. Mukoya

'Yan gudun hijira da ke rarrabe a manyan sansasnoni guda uku a Tanzaniya sun zargi gwamnati da Majalisar Dinkin Duniya da jingine tsarin tallafin ba da kudade da aka fara a baya domin sayen abinci da sauran kayan bukata. Abin da wasu ke cewa ana musu kiwon yunwa kamar yadda Anko Juma ke cewa: "hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki a sansaninmu ba sa tabuka wani abin azo a gani, su na gudanar da ayyukansu tamkar sawun-keke wanda ba a gane gaban shi. Da zarar sun fito da tsarin da jama'a ke murna da shi ba da jima wa ba sai su canza."

Akalla 'yan gudun hijirar Burundi da Kwango dubu 355,000 ke zama a TanzaniyaHoto: DW/Prosper Kwigize

Kwararowar da 'yan gun hijira su ka yi zuwa Tanzaniya a baya-bayannan ya haifar da karin bukatar kudade da gwamnati ke bukata wurin samar da abubuwan more rayuwa kamar yadda Josephat Kataga mukaddashin daraktan majalisar gudanarwa ta yankin Kibondo ya bayyana inda ya ce "a cikin 'yan shekarun nan hakika, hukumomin Majaliasar Dinkin Duniya sun taimaka mana wurin bunkasa kiwon lafiyar jama'a da samar da ruwan sha da kuma gyara muhalli domin dai ba wai 'yan gudun hijira ne kadai ke da matsala ba, akwai sauran jama'ar da ke da bukata."

'Yan gundun hijirar da ke Tanzaniya na fama da matsalolin rashin sukuni da karancin sakewa na neman ayiki a waje da kuma rashin tabbas na samun zaman lafiya a kasashensu na asali.