1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN DA YAN GUDUN HIJIRA KE CIKI A KASAR HOLLAND.

February 13, 2004
A yanzu haka batun mayar da yan gudun hijira izuwa kasashen su shine da yawa daga cikin kasashen turai sukafi mayar da hankalin su kai a halin yanzu.

A misali daga tsakiyar shekarar nan da muke ciki izuwa shekaru uku masu zuwa gwamnatin kasar Holland ta kiyasta mayar da yan gudun hijira dubu asharin da shida izuwa kasashen da suka fito.

Wan nan mataki kuwa da gwamnatin ta Holland ta dauka ya samu goyon bayan da dama daga cikin yan majalisar dokokin kasar,duk kuwa da zanga zangar nuna kyama da yan gudun hijirar keyi a kasar lokaci izuwa lokaci.

Yan gudun hjira kusan dubu biyu da dari biyar ne dai suka gudanar da zanga zanga a kofar ofishin majalisar dokokin kasar don nuna kyama ga wan nan matakin da gwamnatin kasar keson dauka kann yan gudun hijirar.

A lokacin zanga zangar yan gudun hijirar sun bayyana cewa da dama daga cikin su sun dade a kasar ta Holland wanda hakan ke tabbatar musu da yancin zama bi´sa dokart kasa,kuma ma dadin dadawa iodan an mayar dasu kasashen nasu zasu fuskanci hukunci na kisa ne ko kuma dauri.

Bugu da kari nuna kyama dangane da wan nan mataki daga bangaren yan gudun hijirar bai tsaya ga gudanar da zanga zangar lumana ba kawai,domin kuwa har wasan kwaikwayo su kann shirya na nuna rashin jin dadin su da kuma amincewar su da wan nan mataki na mayar dasu kasashen nasu.

Bisa kuwa rahotanni da suka iso mana da dama daga cikin wadanda wan nan mataki na gwamnatin ta Holland ya shafa sun fito ne daga kasashe irin su iraq da Iran da Somalia da Afganistan da Angola da morocco da kuma kasar sin.

A hannu daya kuma yin shakulatin bangaro da koke koken yan gudun hijirar da kuma Mutanen da basu da rinjaye a kasar,a halin yanzu ya jefa kasar cikin halin kaka nikayi na kace nace dangane da wan nan matakin da gwamnatin ta Holland take shirin dauka.

Gwamnatin ta Holland dai ta tabbatar da cewa ta yanke hukuncin daukar wan nan matakin ne bisa hujjar ganin cewa da dama daga cikin kasashen da wadan nan mutane suka fito na cikin zaman lafiya,sabanin zaman dar dar da suka shiga ciki sakamakon yake yake na basasa da kuma ire iren aiyukan yan tawaye.

A yayin da kuwa ake cikin wan nan lamari a hannu daya kuma kungiyoyi na kara hakkin bil adama na kasar na ganin cewa wan nan mataki da kasar ta Holland ke shirin dauka na a matsayin cin zarafin mutanen ne kawai,a don haka suka ce basu ga dalilin daukar wan nan mataki ba a halin yanzu.