Halin da 'yan jarida ke ciki a sassan duniya
May 3, 2018
Ana iya ganin zahirin haka bisa yadda 'yan siyasa na kasashen Turai ke rige-rige aiki da kasar China. Kasar da aka dakile 'yancin 'yan jarida kuma aka toshe kafofin yada labarai kamar tashar DW da sauran na kasashen ketere ko kuma suna sahun baya. Manyan 'yan kasuwa sun fi mayar da hankali kan kasuwanci da China ya zama abin da aka bai wa fifiko maimakon kare hakkin dan Adam. Karkashin haka mahukuntan birnin Beijing suka mamaye komai. Saboda a China babu wanda zai tayar da jijiyar wuya idan aka samu rashin jituwa da masu zuba jari na kasashen ketare.
Wani abun mamaki 'yan siyasa na Jamus da kasashen Turai ke neman ganin an fahimci Shugaba Vladimir Putin na Rasha duk da dari-darin da yake da shi kan kungiyar tsaro ta NATO da Tarayyar Turai. Yayin da tsoron da 'yan jarida ke da shi a daya hannun a Rasha ya zama abin tayar da hankali da ake a boye, don tsoron cin zarafi gami da yiwuwar rasa rai. Sai dai sabon ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya dauki matsaya ta daban.