1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da 'yan mata dalibai da aka sace ke ciki

April 16, 2014

Jami'an tsaro na ci gaba da bincike, yayin da iyaye da masana ilimi suke bayyana alhininsu. Amma har yanzu ba a san inda mata 200 da ake sace suke da kuma yanayin da suke ciki ba..

Afrika Kinder lachen
Hoto: picture-alliance/dpa

.Jami'an tsaro na bayyana cewa suna tsananta bincike don gano inda daliban da aka sace suke yanzu haka. Su dai daliban sun koma makarantar dai bayan da hukumomi suka nemi su komawa domin rubutu jarrabawa kammala karatu. A baya dai hukumomin jihar Borno sun sanar da rufe makarantun bisa dalilai na tsaro.

Iyaye da masu ruwa da tsaki a harkkokin ilimi sun yi roko ga wadanda suka sace wadannan dalibai da su dubi Allah su sakosu ganin mata ne masu kananan shekaru. Labarin sace daliban dai ya ta da hankalin daukacin al'ummar yankin Arewa masu gabashin Najeriya ganin shi ne karon farko da kame mata masu yawa tun lokacin da aka fara rikicin da ake dangantawa da Boko Haram.

Ko ina yaran matan da aka sace su ke?

Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani game da inda yara matan suke, da kuma yanayin da suke ciki. Jami'an tsaro na ci gaba da farauta don gano inda 'yan matan suke. Iyaye na ganin cewa sakaicn mahukanta ne ya sa aka sace wadannan mata 'yan makaranta, musamman ganin irin tarin jami'an tsaro da ake da su a jihar ta Borno.

Iyaye na cikin wani hali bayan sace 'yan mata dalibaiHoto: AMINU ABUBAKAR/AFP/Getty Images

Masharhanta na ganin cewa wannan hali da aka shiga zai iya mayar da hannu agogo baya a fannin ilimi a fannin ilimi. Da ma dai jihohin yankin na sahun gaba na wuraren da ake da karancin ilimi a Najeriya.Yanzu haka dai akwai masu yin roko da a sako 'yan matan ganin cewa suna da karancin shekaru.

Sai dai kuma babu wata kungiya da ta dauki alhakkin sace 'yan mata daliban a jihar Borno. Sai dai hukumomin Najeriya sun zargi kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram da sace daliban da ake ganin cewa sun kai 200.

Mawallafi: Al-Amin Muhammad
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe


Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani