Halin matsananciyar rayuwa ga al'ummar birnin Madaya
January 12, 2016Talla
Dakarun gwamnatin kasar ne dai suka killace birnin na Madaya watanni shida da suka gabata abun da ya haddasa matsananciyar yunwa ga al'umma. 'Yan kungiyar agaji na Red Cressent na kasar ta Siriya sun sanar cewa a kalla manyan motoci 44 cike da kayayakin agaji sun samu shiga birnin a ranar Litinin, inda a cewar kungiyar Médecins sans frontières a kalla mutane 28 sun mutu sakamakon matsananciyar yunwa daga daya ga watan Disamba da ya gabata kawo yanzu.
Ga baki daya dai mutane a kalla dubu 400 ne sojojin na gwamnatin ta Siriya ko kuma mayakan 'yan tawaye suka killace a wannan birnin na Madaya, inda acewar jakadan kasar Spain a Majalisar Dinkin Duniya, killace al'umma domin azabtar da ita da yunwa, na a matsayin babban cin zarafi ga al'ummar.