1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin rashin sanin tabbas a Libiya

March 2, 2011

Yayin da ake ci gaba da gumurzu a yankuna daban daban na Libiya, kotun hukunta laifukan yaƙi ta fara bincike kan zargin aikata laifin cin zarafin mutane a Libiya.

"Amirka da NATO za su ɗanɗana kuɗarsu idan suka tsoma baki a Libiya"Hoto: dapd

A dangane da tashe tashen hankula a Libiya kotun ƙasa da ƙasa dake hukunta manyan laifuka ta fara bincike akan shugaba Muammar Gaddafi da wakilan gwamnatinsa game da aikata ta'asa kan jama'a. Babban mai gabatar da ƙara na kotun, Luis Moreno ya ce binciken farko da suka yi ya ba da madogara bisa wannan manufa. A ranar Asabar da ta gabata Kwamtin Sulhun Majalisa Ɗinkin Duniya ya ba wa kotun dake birnin The Hague izinin yin bincike akan rahotanni game da ta'asar da Gaddafi ke yiwa al'umarsa. A kuma halin da ake ciki shugaban na Libiya ya yi wa Amirka da ƙungiyar ƙawance ta NATO barazanar cewa za su yi asarar dubban sojoji idan dakarun ƙetare suka toma baki a cikin rikicin na Libiya.

A yankuna da dama na gabacin ƙasar ta Libiya ana gwabza ƙazamin faɗa tsakanin magoya baya da 'yan tawaye da Gaddafi. Shaidu sun nunar da cewa faɗa ya ta'allaka ne wajen neman iko da tashoshin man fetir dake kewayen garin Brega. Mutane da dama ne rahotanni suka tabbatar da mutuwarsu. A yau ɗin nan Gaddafi ya bayyana gaban magoya bayansa a birnin Tripolis a wani biki da ya kira na cika shekaru 34 na mulkin jama'a. A jawabinsa cewa yayi nahiyar Turai ce za ta shiga tsaka mai wuya idan al'amura suka dagule a Libiya.

"Wajibi ne ƙawayenmu na Turai da ƙasashen yamma sun fahimci cewa zaman lafiyar Libiya shi ne zaman lumanan yankin tekun Bahar Rum, domin Libiya take daƙile kwararowar miliyoyin baƙin haure da 'yan tarzoma daga arewacin Afirka zuwa Turai."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala