1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin yaɗuwar hayaƙi mai guɓa a Japan

March 15, 2011

Barazanar kamuwa da cututtuka da ke da nasa na iska mai guɓa na daɗa ƙaruwa a Japan kwanaki huɗu bayan girgizar ƙasa da ta lalata tashar nukuliya ta Fukushima.

Tashar makamashin nukiliya ta Fukushima a JapanHoto: AP

Al'amura na daɗa rintsaɓewa a ƙasar Japan bayan lalacewar wani ɓangare na murhun makamashin nukiliyarta da ke irnin Fukushima. Gwamnatin wannan ƙasa ta bayyana cewar barazanar kamuwa da cututtuka na daɗa ƙaruwa, sakamakon bazuwar iska mai guɓa a sararin samaniya da ke fitowa daga sunduƙin da ya fashe. Firaminista Naoto Kan ya bukaci 'yan ƙasar waɗanda matsuguni bai fi tazarar kilometa 30 da cibiyar makamashin da su ƙaurace wa gidajensu, saboda barazanar da ta ke yi ga rayukansu.

Mutane 2400 ne dai aka tabbatar da cewar bala'in girgizar ƙasa da Japan ta fiskanta ya salwantar da rayukansu. Kana bala'in ya na tasiri kan matsayin na biyu na ƙasa da ta fi ƙarfin tattalin arziki a duniya da Japan ke da shi a halin yanzu. Tuni dai kasuwar hada-hadar hannayen jarinta wato NIKKEI wanda ke zama mizani wajen kwantanta karfin tattalin arziki, ta yi faɗuwa ƙasa warwas da kashi 14 daga cikin 100.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala