1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

160811 Kenia Dadaab

August 16, 2011

Dubban 'yan Somaliya na kwarara zuwa sansanin 'yan gudun hijira da ke a kan iyakar ƙasarsu da Kenya domin tsira daga fari tare da samun abinci. Sai dai cunkoso da rashin tsaro na barazana ga rayukansu a garin na Dadaad.

Matan Somaliya da ke gudun hijiraHoto: picture alliance/dpa

Ba abin da ake ji da gani a harabar sansani na Dadaad da ke tsugunar da 'yan gudun hijira da suka fito daga somaliya,illa koke-koken yara ƙanana da kuma hayaniyar iyayen da ke neman yin rejista. Alala haƙiƙa dai galibin mata da ke goyo na kwantar da 'yayansu ne a sararin Allah ta'alah, tare da shafe kwanaki suna layi, kafin a sanya su cikin jerin waɗanda za su dinga samun na sawa a bakin salati. A hakiƙanin gaskiya dai, ɗaruruwan mutane suke tururuwa daga kudancin Somaliya da fari ya addaba zuwa Dadaad na kenya domin samun matsuguni da kuma cimaka. Sai dai Ominde Mobel jami'ar ƙasar Kenya da ke aiki a sansanin, ta ce tafiyar hawainiya da rejistar ke yi ba ya rasa nasaba da mummunan halin da 'yan Somaliya ke isowa a ciki.

Rabon abinci ga 'yan gudun hijiran SomaliyaHoto: dapd

"Muna iya ƙoƙarin mu. Muna kuma nema a yi mana aiki gafara game da nawan da ake fiskanta. Hasali ma su 'yan gudun hijiran na cikin wani mummanan yanayi. da dama daga cikin su ba su da koshin lafiya. kana sun yi rasa 'yaya da 'yan uwa. ba su da mastuguni, ba su dai komai na rayuwa."

Adadin waɗanda 'yunwa ke addaba a kudancin Somaliya

Mutane miliyon biyu da ke fama da ja'ibar 'yunwa a kudancin Somaliya ne ke neman yi hijira zuwa sansanin Dadaad na kenya, saboda ƙafar angula da ƙungiyar al-Shabaab ke ci gaba da yi wa shirin raba abinci ga mabukata. Lamarin da ke sa 'yan somaliyan ke shafe kwanaki suna taka sayyada kafin sun iso wannan sansani a cewar ɗaya daga cikinsu.

"Halin da ake ciki a somaliya dai sai gyaran Allah. Mun yi asarar ɗaukacin dabobbinmu. shi ya sa na zo nan. Kwanaki huɗu na shafe akan hanya kafin in iso wannan sansani. Sai dai a kan hanya, 'yan fashi sun ƙwace ragowar abin da na mallaka."

'Yan somaliyan dai na isowa sansanin ne a gajiye, ba tare da kuma sisin kwabo a aljuhu ba. Tufafin da wasu daga cikinsu suka sanya ba sa rufe al'awarsu saboda lalacewa da suka yi. wasu 'yan gudun hijiran na somaliya ma ba sa samun tanti da za su sa hakarkarinsu idan dare ya yi, sakamakon cika da batsewar da sansanin da ke kan iyakar Kenya da somaliya ya yi. To amma a cewar Enoch Ochola, shugaban ayyukan jin ƙai na hukumar 'yan gudun hijira ta duniya, sun fara lalaɓo hanyoyin faɗaɗa sansanin.

Jigilar abinci zuwa ƙasashen doron Afirka da ke fama da 'yunwaHoto: dapd

" Sansanonin uku na Dadaad, an tanade su domin sun ƙunshi kimanin mutane dubu 90. Amma kuma rikicin da ƙasar Somaliya ta shafe shekaru 20 tana fiskanta ya haddasa ƙaruwar 'yan gudun hijira. A yanzu dole ne mu tari karin mutane dubu 400.  Muna tattaunawa da gwamnatin Kenya domin ta samar mana wasu waurare da za mu tsugunar da waɗanda ke isowa, baya ga sansanoni ukun da ake da su."

Halin tsaro a sansanin Dadaad na ƙasar Kenya

'Yan Somliayan dubu 15 ne aka tsugunar a ɗaya daga cikin sansanonin da harkar tsaro ba shi tabbasa a ciki. Babu jami'an tsaro da ke zirga zira. Saboda haka ne mata suka fiskantar cikin zarafi iri daban daban ciki har da fyaɗe kamar yadda ɗaya daga cikinsu ta bayyana.

"An yi wa 'yayanmu mata fyaɗe, an sace ɗan abin da muka mallaka. ba za mu iya rayuwa a cikin wannan yanayi ba. mun gwamace mu koma somaliya domin a can munada matsuguni."


 Sai dai 'yan somaliya  da suka kwan biyu a sansanin 'yan gudun hijira na Dadaad, suka ce ba mafarkin komawa ƙasarsu ta asali domin kuwa ta na cikin halin gaba kura baya siyaki: ma'ana baya ga yaƙi, fari ya zo ya afka ma ta.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Usman shehu Usman