Hamas da Fatah sun ƙudurci girka gwamnatin riƙwan ƙwarya
September 12, 2006Ƙungiyoyin Fatah da na Hamas na ci gaba da tantanawa a yunƙurin girka, gwamnatin haɗin kasa a Palestinu, da ta ƙunshi ɓangarorin 2.
Babban burin wannan gwamnati shine na samar da haɗin kai bayan rigingimun da su ka ɓarke tsakanninmagoya bayan hamsa da na Fatah a kwanakin baya.
Kazalika, su na masu buƙatar cimma nasara, cire takunkumi da ƙasashen turai da Amurika, su ka sakawa Palestinawa, tun watan Janairu da ya gabata, a sakamakon rinjaye, da Hamas ta samu, a Majalisar Dokoki.
A nasa ɓangare, tunni, shugaban hukumar palestinawa Mahamud Abbas, ya alƙawartawa ma´aikatan gwamnati, biyan bassukan albashin watani 6, da su ka tambayo, bayan girka sabuwar gwamnatin.
Ƙungiyar gamayya turai, a cikin sanarwar da ta hiddo, ta yi lalle marhabin, da shawara da Palestniawa su ka yanke, ta girka gwamnatin haɗin kan ƙasar.
Itama Isra´ila, ta bada sanarwar belin wasu daga yan majalisun dokoki, da ministocin Hamas da ta kame, a yunƙurin ceton sojan ta ɗaya, da a ke ci gaba da garkuwa da shi, a zirin gaza.