1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas na ci gaba da nuna iko a zirin Gaza

Mahmud Yaya Azare
October 15, 2025

Bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila mayakan Hamas sun fara farautar wadanda suka kira karnukan farautar Isra'ila a zirin.

'Yan kungiyar Hamas na ci gaba da nuna tasiri a Gaza
'Yan kungiyar Hamas na ci gaba da nuna tasiri a GazaHoto: Jehad Alshrafi/AP Photo/picture alliance

Mayakan kungiyar Hamas sanye da bakaken tufafi da suka rufe fuskokinsu suna zartar da hukuncin kisa a bainar jama'a  ga wasu daga cikin mambobin kungiyar Abu Shabab da ke samun tallafin Isra'ila,wadanda suka fito karara suna yakar kungiyar ta Hamas da nufin ganin bayan mulkinta a Gaza .

 A jajiberen ranar da aka cimma yarjejeniyar dakatar da yaki a Gaza ne kungiyar ta Abu Shabab da ke da mabiya, ta kashe Abu Ja'afar wani babban kwamandan mayakan Hamas da Isra'ila ke nema ruwan a jallo.

Wasu Falasdin awa a Gaza bayan tsagaita wutaHoto: Ebrahim Hajjaj/REUTERS

Tun da aka fara batun tattaunawar zaman lafiya a Gaza ne dai jagororin kungiyar ta Abu Shabab suka fara yin kamun kafar Isra'ila da ta tabbatar musu da tsaron lafiyar su da ta iyalansu kafin cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Hamas da janyewar dakarunta daga Gaza.

 Dr Ateef Bisharah mai sharhi kan rikin Isra'ila da Falasdinawa, ya ce ba abun mamanki bane don Isra'ila ta jefar da ganga bayan ta ci moriyarta:

"Har zuwa ranar da aka kawo karshen yaki, wadannan maciya ammanar na ci gaba da kakkashe jagororin Hamas da sauran kungiyoyin gwagwarmaya tare da hadin guiwar da suke da dakarun sojin dana leken asirin Isra'ila, don an yi musu alkawarin danka musu mulki bayan an gama da Hamas bayan yaki. Na yi ammanar cewa, kamar yadda Isra'ila ta ci ammanar Mahmud Abbas duk da irin hidimtawar da yayi wajen murkushe 'yan gwagwarmaya, babu wanda ba za ta yi wa ingiza mai kantu ruwa ba don gwara kan Falasdinawa da rura wutar gaba a tsakaninmu."

 To sai dai kamar yadda Sharon Blety, tsohon jami'n hukumar leken asirin Isra'ila ke cewa, har abada Isra'ila ba za ta yi watsi da wadanda suka hidimta mata ba:

Fara gyara wuraren da Israila ta lalata a GazaHoto: Ebrahim Hajjaj/REUTERS

"Na yi ammanar cewa, jagororin kungiyar Abu Shabab da suka yi aiki damu suna nan cikin koshin lafiya da cikakken tsaro. Shi kansa wannan kashe karshen da Hamas ke yi a yanzu, wani sako ne da muke isarwa duniya don sake matsa lamba a gama ganin bayan ta a yankin da ake shirin jibge rundunar sojin kasa da kasa a cikinsa."

A daura da haka, mazauna zirin Gaza da ke komawa gidajensu da aka ragargaza a yaki, na ci gaba da amfani da hannayensu, saboda karancin kayayyakin aiki, don gyara matsugunai a baraguzan gidajensu lamarin da ke nuni aa irin jajircewarsu ta ci gaba da zama a yankin ko ana muzuru ana shaho.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani