Kungiyar Hamas ta amince da wasu kudurori da Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar domin kawo karshen yakin Gaza.
Buraguzan gine-gine a GazaHoto: Saeed M. M. T. Jaras/Anadolu Agency/IMAGO
Talla
Mayakan na Hamas sun kuma amince da mika dukkan fursunonin yakin Isra'ila da ke raye tare kuma da dukkan gawarwakin wadanda suka mutu a hannunsu ga hukumomin Tel Aviv. Kazalika kungiyar ta ce za ta shiga cikin tattaunawar wanzar da zaman lafiyar yankin tare kuma da yin nazari kan daftarin da Trump ya gabatar.
Al'ummar Gaza a karon farko sun wayi gari cikin farin ciki ba tare da jin rugugi daga sararin samaniyar yankin ba, inda haske ya mamaye sararin samaniyar Gaza a wannan Asabar ba tare da duhun hayakin bama-bamai da makamai masu linzami ba, biyo bayan daftarin da Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar na kawo karshen luguden wutan da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza.
Jamila al-Sayyid daya daga cikin al'ummar Gaza ta ce tayi matukar mamakin matakin da Trump ya dauka na tsagaita bude wuta, kasancewar a kullum yana tare da Isra'ila, haka shi ma wani mazaunin yankin Mahmud Abu Shamala, ya ce tsagaita wutar ya zo masa tamkar a mafarki to amma hannun agogo na iya komawa baya idan har Hamas bata saki dukkan fursunonin yakin Isra'ila ba.
Shugaba Donald Trump na Amurka a yayin da ya karbi bakwancin Benjamin NetanjahuHoto: Jim LoScalzo/CNP/AdMedia/picture alliance
Kudurorin Trump guda 20 kan yankin na Gaza sun hadar da dakatar da tsagaita bude wuta nan take da musayar fursunonin yakin bangarorin biyu da kuma janyewar dakarun Isra"ila daga Gaza sauran kudurorin sun hada da kwance damarar makaman Hamas da kuma nada kantoman da zai jagoranci sake gina yankin, sannan kuma shugaban Donald Trump ya yi kira ga kungiyar Hamas da ta gaggauta amincewa da bukatar zaman lafiyar yankin ko kuma ya murkushe kungiyar.
Hamas da kasashen duniya ciki har da Amurka da Jamus da Tarayyar Turai ke yi wa kallon yar ta'adda na rike da 'yan Isra'ila akalla 48 da ake hasashen 20 daga cikinsu na raye. Tuni dai kungiyar Hamas ta amince da bukatar zama a teburin sulhu tare da amincewa da sakin dukkan fursunonin yakin Isra'ila.
A cikin buraguzan gine-ginen Zirin Gaza, matasan makada na rike da jita da sauran kayan kida. Suna samar da yanayi na fata da martaba, a daidai lokacin da ake fama da yunwa da rashi da kuma cutar tsananin firgici.
Hoto: Dawoud Abu Alkas/REUTERS
Hada hannu waje guda, domin yakar firgici
Kwalejin Gaza, makaranta a birnin Gaza. Harsashi ya farfasa bangon gine-ginen gidaje, yayin da tagogi suka tarwatse. A nan yara mata uku tare da namiji guda na zaune suna koyon kada jita, tare da malaminsu Mohammed Abu Mahadi. Malaminsu ya yi imanin kida zai taimaki lafiyar kwakwalen mazauna Zirin Gaza, daga firgicin tashin bama-bamai da zafin ciwuka da yunwa da rashin 'yanci.
Hoto: Dawoud Abu Alkas/REUTERS
Ci gaba da koyarwa
A farkon shekara ta 2024, Ahmed Abu Amsha malami ne da ke koyar da kidan jita da sauran kayan kida, ya kasance guda daga cikin malaman farko cikin malamai da daliban makarantar koyon kida ta Edward Said National Conservatory of Music da suka fara bayar da darasin koyon kida a yankin kudancin Gaza da yaki ya dai-daita. A yanzu ya sake komawa yankin arewacin birnin Gaza da zama.
Hoto: Dawoud Abu Alkas/REUTERS
'Kida na sanya mini kyakkyawan fata'
"Kida na sanya mini kyakkyawan fata da rage min firgici," a cewar Rifan al-Qassas mai shekaru 15 a duniya da ta fara koyon kidan (oud) wato jita ta gargajiya ta Larabawa tun tana shekaru tara. Al-Qassas na fatan kada jitarta a kasar waje. Al'umma na cikin fargabar kora daga Gaza, saboda matakin majalisar zartaswar Isra'ila na ranar takwas ga watan Agustan 2025 na kwace iko da yankin Zirin Gaza.
Hoto: Dawoud Abu Alkas/REUTERS
A cikin mafi munin yanayi
A gaban tantin malaman da ke koyar da kidan, akwai baraguzan gine-gine da suka rushe a birnin Gaza. Kusan gaba dayan al'ummar yankin na cikin tantunan gaggawa ne. Akwai karancin abinci da tsabtataccen ruwan sha da magunguna. Dalibai da malamansu na ba su da karsashi saboda yunwa. Wasunsu da kyar suke samun damar zuwa azuzuwansu.
Hoto: Dawoud Abu Alkas/REUTERS
Wani abu mai kyau da zai sassauta radadin mutuwa da wahalhalu
Bafalasdine Youssef Saad tsaye tare da jitarsa, a jikin ginin makarantar da yaki ya tarwatsa. Kayan kida kalilan ne suka tsira a rikicin. Tuni Youssef da ke da shekaru 18 a duniya, ke da babban fata: "Ina fatan zan iya koyar da yara kida, ta yadda za su ga haske duk da yanayin yaki."
Hoto: Dawoud Abu Alkas/REUTERS
Lokacin nuna basira
Duk mummunan yanayin da ake ciki, koyon kada kayan kade-kade na samun halartar 'yan kallo. Cikin tanti, daliban da ke koyon kidan na nuna kwarewarsu, yayin da 'yan kallo ke tafa musu. Kayan kidan na tashi, inda suke cimma dogon zango yayin da aka kada su. Mai shekaru 20 da ke koyon kidan jita ya bayyana cewa: "Ina son sanin sababbin salon kade-kade, musamman mai karfi, ina son kida mai amo.
Hoto: Dawoud Abu Alkas/REUTERS
Lokacin farin ciki
Waka ma na taka muhimmiyar rawa. Yadda muryoyin yaran ke tashi na da dadin sauraro, sabanin karar abubuwa masu fashewa da bama-bamai da ke yin kisa da al'ummar yankin Zirin Gaza suka saba ji yau da kullum.
Hoto: Dawoud Abu Alkas/REUTERS
Kida domin magance ciwo
Osama Jahjouh na busa sarewa da ake amfani da ita a kade-kaden Larabawa da Iraniyawa da kuma Turkawa. ya ce: "Wasu lokutan ina dogaro da salon horon numfashi ko kuma in zauna shuru ina busawa, idan karar habe-harbe da tashin bama-bamai suka yawaita. Idan ina yin busa, ina jin kamar zan iya sake yin numfashi, kamar sarewar na magance min ciwon da nake ji a cikin jikina."