Hamas ta mayar da wuraren Fatah dake Gaza ƙarƙahin ikon ta
June 14, 2007Talla
A dangane da rikici mai kama da yakin basasa da ke kara yin muni tsakanin kungiyoyin Falasdinawa da ba sa ga maciji da juna, shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da FM Isma´il Haniya sun yi kira da a kawo karshen tashe tashen hankukla a Zirin Gaza. Sun yi kira ga magoya bayansu da su daina fada nan take. Da farko kungiyar Hamas ta mayar da wurare da dama a Zirin na Gaza karkashin ikonta bayan ta mamaye kusan dukkan hedkwatocin jami´an tsaro dake da alaka da Fatah. Sojojin sa kai na Hamas sun mamaye birnin Khan Yunis sannan suna ci-gaba da dannawa zuwa Rafah dake kudancin yankin. Akalla mutane 60 aka kashe a fadan da aka kwashe kwanaki ana yi a yankin na Falasdinawa.