1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Hamas ta rusa gwamnatinta a Gaza

Abdul-raheem Hassan
July 6, 2026

Bayan shafe shekaru kusan 20 tana mulki a Gaza, kungiyar Hamas ta amince da mika ragamar gwamnatin yankin ga kwamitin kwararru ta Falasdinu ta 'yan ba ruwanta da siyasa. Matakin zai bude kofar sake gina yankin.

Wani dan Gaza yana tsaye a tsakiyar baraguzan gini
Wani dan Gaza yana tsaye a tsakiyar baraguzan giniHoto: Dawoud Abu Alkas/REUTERS

Sanarwar ta fito ne bayan wani taron manema labarai da kakakin gwamnatin Hamas, Ismail al-Thawabta, ya gudanar a Deir al-Balah. Inda ya bayyana cewa an yanke shawarar rushe kwamitin gwamnatin Gaza tare da nada wani mutum da kowa zai amince da shi domin kula da harkokin gwamnatin na wucin gadi har sai sabon kwamitin gudanar da mulkin Gaza ya karbi aikinsa gaba daya.

A cewar Hamas, ma'aikatan gwamnati da kwararrun jami'an gudanarwa za su ci gaba da aikinsu na yau da kullum domin tabbatar da cewa ayyukan gwamnati ba su tsaya ba, yayin da ake gudanar da sauyin mulkin. Sai dai kungiyar ba ta bayyana takamaiman ranar da za a kammala mika mulki ba.

Hamas ta karbi ragama da ikon zirin Gaza tun a shekarar 2007 bayan rikici da kungiyar Fatah, kuma tun daga lokacin take tafiyar da harkokin mulki a yankin. Sai dai yakin da ya dade tsakanin Hamas da Isra'ila ya haddasa mummunar barna a Gaza, lamarin da ya kara matsin lamba na neman sabon tsarin gudanarwa da zai saukaka sake gina yankin da kuma inganta rayuwar fararen hula.

Masu nazarin siyasa na ganin wannan mataki na Hamas na iya zama muhimmin ci gaba wajen aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma bai wa sabon kwamitin kwararrun Falasdinawa damar jagorantar ayyukan farfado da Gaza. Sai dai sun yi gargadin cewa har yanzu akwai man'yan batutuwa da ba a warware ba, musamman kan makomar makaman Hamas da tsaro da kuma yadda za a tabbatar da cikakken mika ikon gudanar da mulki.

A halin yanzu, ana ci gaba da tattaunawa tsakanin masu shiga tsakani da bangarorin rikicin, domin tabbatar da dorewar tsagaita bude wuta da kuma kammala shirye-shiryen kafa sabon tsarin gudanar da harkokin Gaza.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW