1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ta sako dan Amurka da ta tsare a Gaza

Abdullahi Tanko Bala
May 12, 2025

Hamas ta sako wani dan Israila kuma dan Amurka Edan Alexander da ta tsare a zirin Gaza tsawon watanni 19 a wani mataki na yunkurin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Israila

Matashi Edan Alexander da Hamas ta sako
Hoto: Oded Balilty/AP/picture alliance

Matashin mai shekaru 21 an mika shi ga kungiyar agaji ta Red Cross a kudancin Khan Younis.

Alexander wanda ke aiki da sojin Israila a lokacin da aka yi garkuwa da shi, shi ne mutum na karshe da aka sani dan Amurka da ya rage a raye daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a Gaza.

An sami damar sako shi ne bayan tattaunawa tsakanin Hamas da Amurka ba tare da sanya bakin Israila ba.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce gwamnatinsa ta jinjina wa dawowar Edan Alexander wanda mayakan Hamas suka tsare a Gaza tun watan Oktoban 2023.