Hamas ta sako mutane 17 a mataki na 3 na musaya da Isra'ila
November 27, 2023Kungiyar Hamas ta sako mutane 17 a Lahadin nan, a mataki na uku na musayar fursunoni tsakaninta da Isra'ila, da suka hada da Isra'ilawa 14 da Ba-Amurke daya, yayin da ita kuma Isra'ilar ta sako Falasdinawa 39 dukkansu maza daga kurkukunta, wadanda shekarunsu suka kama daga 15 zuwa 19.
Karin bayani:Kwamandojin Hamas 4 sun mutu a Gaza
Yarjeniyar dai ta fara aiki ne a ranar juma'ar da ta gabata, bayan amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 4 a yakin Zirin Gaza, inda masu shiga tsakani wato Qatar da Masar da kuma Amurka ke fatan tsawaita ta.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce shugaba Joe Biden na Amurka ya bukace shi da ya amince da tsawaita wa'adin tsagaita wutar, to sai dai ya shaida masa cewa da zarar wannan wa'adi ya kare sojojinsa za su koma fagen daga don ci gaba da kai hare-hare Gaza.
Karin bayani:Za a sako karin mutanen a Gaza da Isra'ila
Rikicin dai ya yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa kusan da dubu goma sha biyar, da kuma Isra'ilawa dubu daya da dari hudu.