Ganawar wakilan Turai da Abdallah Hamdok
October 28, 2021Wakilan kasashen Jamus da Faransa da Britaniya da kuma Amirka da suka gana da Abdallah Hamdok da sojoji suka sake a jiya Laraba bayan yi masa daurin talala biyo bayan rusa gwamnatin da yake jagoranta, sun ce sun same shi cikin koshin lafiya. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Amirka da sauran kasashen duniya ke kara matsa kaimi don ganin an maido da gwamnatin farar hula a kasar ta Sudan da ta fada cikin rikici a sakamakon juyin mulki.
Sakataren harkokin wajen Amirka Anthony Blinken, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter a wannan Alhamis, ya ce, sun tattauna ta wayar tarho da Ministar harkokin wajen kasar, Mariam Sadiq al-Mahdi, a game da mayar da ragamar mulkin kasar hannun farar hula kamar yadda 'yan kasa suka nemi a yi a tsawon kwanakin da suka kwashe suna zanga-zangar adawa da juyin mulkin.
Janar Abdulfattah al-Burhan da ake zargi da jagorantar juyin mulkin bayan rusa majalisar koli ta rikon kwarya da Firaiminista Abdallah Hamdok ke jagoranta. Yanzu Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta dakatar da Sudan daga cikin jerin membobinta har sai an dawo da gwamnatin da sojoji suka rusa.