Masu mulki na muzgunawa 'yan adawa a Afirka
November 26, 2026
'Yan siyasa 'yan adawa da manazarta al'amuransiyasa s un ce cin zarafi da yi wa 'yan adawa tarnaki sun sa kalubalantar masu rike da madafan iko yana da matukar wahala. Shin wani sabon yanayi ne yake bullowa a yanzu?
Daga Kamaru da Tanzaniya da Mozambik da Najeriyada Zambiya shugabannin adawa sun zargi hukumomi da tauye musu 'yancin gudanar da harkokinsu na siyasa ta hanyar amfani da dokoki.
A kowane hali dai, jami'ai sun ce matakan na da hurumi a karkashin dokokin kasa da kuma matakan tsaro.
Ngam Glory Ani Mbom 'yar kasar Kamaru, ta ce Kamaru na da sarkakiya kuma yana da muhimmanci mu san lokaci da ya dace a soki gwamnati da kuma lokacin da bai dace a soki gwamnatin karara ba a fili.
Ta ce fargabar kamu na jami'an tsaro da tashin hankali suna saregwiwar harkokin siyasa...
"Ta ce ba za ka iya cewa komai a kan Dimukuradiyya ba idan har ba za a sakar wa yan adawa mara su baiyana ra'ayoyinsu a fili da fadin abubuwan da ke zukatansu ba".
Sai dai ga Nda Grimbald mataimakin sakatare janar na Jam'iyyar adawa ta Social Democrat ic Front a Kamaru, daya daga cikin manyan kalubale shi ne iya gudanar da taruka a bainar Jama'a.
"Ya ce babban kalubale na farko da muke fuskanta a matsayin 'yan adawa shi ne hana mu izinin gudanar da taruka a filayen wasanni da dakunan taro na jama'a. Sannan 'yan adawa ba a fiye sauraron shawarwarinsu ba a majalisar dokoki.
Dokokin Kamaru sun bayar da damar gudanar da tarukan jama'a a waje guda kuma dokokin sun bayar da dama ga hukumomi su takaita tarukan kan togaciyar hana tarzoma da kuma tsaron kasa. Sannan ana bukatar masu shirya taron su sanar da jami'ai kafin lokacin taron.
A Tanzania jagoran adawa Tundu Lissu an kamashi a watan Afrilun 2025 kan tuhumar cin amanar kasa. A watan Nuwamba babbar kotun tarayya ta wanke shi daga zargin cin amanar kasa amma ta ce ta same shi da laifin tunzura jama'a ta yanke masa hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari.
A Mozambique, shugaban 'yan adawa Venancio Mondlane na fuskantar tuhumar laifuka guda biyar da ke da nasaba da zanga-zanga bayan takaddamar zaben 2024 ciki har da zargin tunzura jama'a su aikata ta'addanci. Mondlane ya musanta zargi.
A Zambia ma, jagoran adawa Brian Mundubile ya yi suka kan abinda ya kira koma bayan 'yancin Dimukuradiyya. Kotun ta tafi hutu a ranar 24 ga wata, da ke ranar karshe ta karbar korafin kan zaben shugaban kasar.
A Najeriya kuwa 'yan sanda a jihar Borno sun kama mutane biyar saboda sanya taguwa da aka rubuta wa take "Tinubu Must Go" Dole Tinubu ya tafi. 'Yan sanda sun ce ba a kama mutanen saboda dalilai na siyasa ba amma an kama su ne saboda zarginsu da kwayoyi da sauran laifuka da suka hada da tada hankalin jama'a da kuma daba. A Kano, 'yan sanda sun toshe hanyoyin zuwa wani taro inda suka yi togaciya da damuwar tsaro: