Hana saka matasa aikin tarzoma a Faransa
December 15, 2014Talla
Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ce da sanyin safiyar Litinin din nan ce 'yan sandan suka afka wa wurare da dama a fadin kasar musamman ma birnin Paris da Toulouse da kuma Normandy.
Ya zuwa yanzu dai ba a yi karin haske ba game da adadin wadanda aka kama sakamakon sumamen. Da ma dai jami'an tsaro da ma hukumomin Faransa sun jima suna nuna fargabarsu dangane da yadda suka ce matasa a kasar na shiga ayyuka na tarzoma.