1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Zabe da kalubalen dimukuradiyya a Côte d' Ivoire

Mouhamadou Awal Balarabe
October 24, 2025

Yayin da Côte d' Ivoire ke fuskantar babban zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Oktoba, 'yan takara biyar da ke fafatawa a tsakaninsu na kiraye-kirayen sansantawa tsakanin bangarorin da ke gaba da juna

Shugaba Alassane Ouattara na Jam'iyyar RHDP yayin yakin neman zabe
Shugaba Alassane Ouattara na Jam'iyyar RHDP yayin yakin neman zabeHoto: Joseph Zahui/Matrix Images/IMAGO

Zaben shugaban kasar Côte d' Ivoire na gudana ne a daidai lokacin da aka shafe shekaru goma na kwanciyar hankali bayan rikicin da ya biyo bayan zaben 2010-2011, wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da raba kan al'ummar kasar ta yammacin Afirka. A halin yanzu ma dai, a yayin da Côte d'Ivoire ke ci gaba da samun bunkasar tattalin arziki, har yanzu akwai rikice-rikice da ake fuskanta a fagen siyasar kasar.

Karin Bayani: Gwamnatin Côte d'Ivoire na murkushe 'yan adawa- Amnesty

Idan babu dan takara da ya samu sama da kashi 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada, 'yan takara biyu da suka fi samun kuri'u za su haye zagaye na biyu, lamarin da mai yiyuwa ya kara dagula fagen siyasa da haifar da rashin tabbas a zamantakewar kasar na tsawon makonni masu zuwa. Alal hakika ma dai, dan takarar da aka zaba a mukami mafi daraja a Côte d' Ivoire zai yi wa'adin shugabanci na shekaru biyar, inda zai tsara alkiblar siyasar kasar na sauran shekaru goma idan ya samu wani sabon wa'adi na shugabancin kasa.

Ouattara na neman wa'adi na hudu

Shugaba Alassane Ouattara na Jam'iyyar RHDP yayin yakin neman zabeHoto: Joseph Zahui/Matrix Images/IMAGO

Shugaba Alassane Ouattara, mai shekaru 83, na neman wa'adi na hudu bayan sauya kundin tsarin mulkin kasar a shekarar 2016 da ta soke shingen iyakance wa'adin mulkin biyu kacal. Ana ma sa ran tsohon masanin tattalin arziki na IMF, Ouattara, ya yi nasara a zaben, saboda a karkashin jagorancinsa, Côte d'Ivoire ta zama daya daga cikin kasashe masu saurin bunkasar tattalin arziki a nahiyar Afirka, sakamakon zuba jari da samar da ababen more rayuwa.

 A cewar Bankin Duniya, "Cote d'Ivoire ta samu ci-gaba mafi sauri a yankin kudu da hamadar Sahara na fiye da shekaru goma." Ko da a tsakanin 2012 da 2019, bunkasar tattalin arzikin kasar ta karu da akalla kashi 8.2%, kuma ko da lokacin annobar cutar COVID-19, kasar ta samu ci gaba mai ma'ana a fannoni da dama. Hasali ma dai, yankin Daloa da ya yi fice a harkar noma amma ba shi da masana'antu ya kasance abin misali, inda shirin PRICI na gwamnati ya inganta ababen more rayuwa kama daga  hanyoyi zuwa samar da ruwa da tsaftar muhalli, da sauran gine-ginen asibitoci da makarantu.

Karin Bayani: Rudani gabanin zaben kasar Cote d'Ivoire

Sai dai har yanzu akwai kalubale da ke gaban gwamnati, saboda kashi 25% na hanyoyin Daloa ne kawai aka wadata da kwalta a Côte d' Ivoire. A halin yanzu ma dai, babu kwalta a tsawon kilomita 191 da ke hade Daloa zuwa Vavoua, Séguéla, da Kani, lamarin da ke bakanta ran Yaya Sanogo, wani tela a garin Vavoua.

Alassane Ouattara a wani taron gangamin Hoto: Sia Kambou/AFP

"Hanyar ba ta da kyau; koda zirga-zirga za ka yi akwai matsala. Ba ma iya gudanar da ayyukanmu kamar yadda muka saba. Ina sanye da farar riga a yau, kuma zan yi tuki, amma hanyar ba ta da kyau. Dole ne in yi tuki a hankali."

'Yan adawa na fuskantar tsana

Matakin da Ouattara ya dauka na sake tsayawa takara a jam'iyyarsa ta RHDP, ya sake haifar da wata muhawara da aka saba yi game da kayyade wa'adin mulki da kuma tabbatar da dimukuradiyya. An haramta wa wasu fitattun ‘yan adawa tsayawa takara ciki har da tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo, da tsohon firaminista Guillaume Soro, da tsohon shugaban matasa Charles Blé Goudé da Tidjane Thiam, tsohon shugaban kamfanin Credit Suisse. Sai dai wannan wariyar ta haifar da suka da damuwa game da sahihancin tsarin zaben Côte d' Ivoire. Amma maimakon martani kan sukar da ake masa, Ouattara ya yi alkawarin samar da babbar hanyar da ta hada Daloa zuwa Yamoussoukro babban birnin kasar.

"Muna farin cikin farawa da Daloa, yanki mai wadata da zai iya ba da gudunmawa mai yawa ga ci-gaban Côte d'Ivoire. Na tabbata za mu yi abin da ya fi na baya. Muna shiga wa'adin 2025-2030 da karsashi mai yawa saboda muna da tabbacin cewa ci-gaban zai kasance mai karfi. Za a samu karin ababen more rayuwa, da ingantaccen yanayin rayuwa ga kowane dan kasa. Ina so in fada a nan a nan Daloa cewa kowa ya kamata ya fahimta: Muna kan yanayi mai kyau, abubuwa za su inganta, kuma muna kan hanya madaidaiciya."

Mata ‘yan takara sun ci gaba

Hoton 'yar takarar shugaban kasar Ivory Coast Simone Ehivet Gbagbo a yakin neman zabeHoto: Joseph Zahui/Matrix Images/IMAGO

A bangaren mata kuwa, Simone Ehivet Gbagbo, tsohuwar uwargidan shugaban kasa wacce ta dade tana siyasa, tana mayar da hankali kan ilimi, da sake fasalin zamantakewa da sakar wa kananan hukumomi mara.

Ita ma Henriette Lagou Adjoua, tsohuwar ministar harkokin mata da ta tsaya takara, ta yi alkawarin ba da kariya mai karfi na doka da shan alwashin aiwatar da dokar samar wa mata kaso 30% na mukamai, saboda tana ganin cewar ana mayar da mata saniyar ware a Côte d' Ivoire.

" Batu ne na karfafa mata, batu ne game da daidaiton jinsi. Ka ga an mayar da mata saniyar ware. A halin yanzu, muna da doka da ta tanadi kashi 30 cikin 100 na mukamai ga mata, amma ba mu gamsu ba. Shi ya sa na tsaya takara. Idan na yi nasara a  ranar 25 ga watan Oktoba, za a aiwatar da cikakken tsari domin daidaiton jinsi ya yi nasara."

Muryoyi masu zaman kansu

Dan takarar adawa Jean-Louis Billon wajen yamkin neman zabeHoto: Joseph Zahui/Matrix Images/IMAGO

Jean-Louis Billon, dan kasuwa ne kuma tsohon minista, yana fafutukar ganin an inganta da zamanantar da tattalin arzikin Côte d'Ivoire tare da rage rashin aikin yi da bunkasar kamfanoni masu zaman kansu. Shi kuwa Ahoua Don Mello, mataimakin shugaban jam'iyyar PPA-CI, ya sa abubuwan da ya sa a gaba, ciki har da sake fasalin dimukuradiyya, da tsarin tattalin arziki, da samar wa Côte d' Ivoire cikakken 'yanci tare da yin afuwa ga fursunonin siyasa.

Tsaro da labarin bogi

Rashin zaman lafiya a yankin yammacin Afirka musamman a Burkina Faso, Mali, da Guinea ya sanya tsaro ya zama babban batu a kasar Côte d' Ivoire. Gwamnati ta kaddamar da "Operation Espoir", inda ta tura jami'an tsaro 44,000 tare da haramta zanga-zanga, da nufin hana tashe-tashen hankula da tabbatar da zaman lafiya a lokacin zabe. Sai dai masu sukar matakin suka ce wannan yana takaita gangamin 'yan takarar adawa da gudanar da muhawara a tsakanin jama'a.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta soki matakin hana gudanar da zanga-zangar lumana, inda ta bayyana shi da tauyen ‘yancin walwala da ka’idojin demukuradiyya.