1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Hanoi: Ambaliya ta hallaka mutane fiye da 150

Abdullahi Tanko Bala
September 11, 2024

Hukumomi a a Hanoi na neman mutanen da suka bace bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da ta haddasa ambaliya da zaftarewar kasa.

Vietnam | Ambaliyar ruwa
Hoto: Thinh Nguyen/REUTERS

An kwashe dubban mutane daga Hanoi babban birnin kasar Vietnam a sakamako guguwa mai karfi hade da ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi wa lakabi da guguwar Yagi da ta hallaka mutane fiye da 150.

Hukumar kula da yanayi ta ce kogin Hanoi ya cika makil wanda ba a taba ganin irinsa cikin shekaru ashirin da suka gabata, lamarin da ke barazana ga mazauna gabar kogin.

Wani Jami'in dan sanda a Hanoi ya ce suna aikin kwashe mutane zuwa matsugunai na wucin gadi ko kuma inda za su zauna tare da iyalai. Yace ruwan ya yi yawa kuma ana hasashen samun karin ruwan sama.

Kafar yada labaran kasar ta ce tumbatsar kogin Yagi ya haddasa zaftarewar kasa a wani kauye da yankin tsaunuka inda mutane 22 suka rasa rayukansu. Gwamnatin ta yi kiyasin cewa akwai mutane kimanin 140 da suka bace har yanzu ba a gano su ba.