1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hanyar da sojin ECOWAS za su bi wajen inganta tsaro

Uwais Abubakar Idris MAB
August 8, 2024

Hafsoshin soji na kasashen yankin Afrika ta Yamma sun yi taro a Abujan Najeriya inda suka tattauna kalubalen rashin tsaro da juyin mulki da watsuwar kanana makamai a hannun fararen hula a yankin da ECOWAS ke da iko.

Hafsoshin sojin kasashen Ecowas/cedeao sun saba taruwa a Abuja babban birnin Najeriya
Hafsoshin sojin kasashen Ecowas/cedeao sun saba taruwa a Abuja babban birnin NajeriyaHoto: Chinedu Asadu/AP Photo/picture alliance

Guguwar sauya gwamnati ta amfani da karfin bindiga na soja ne kan gaba wajen batutuwan da manyan hasoshin tsaron na kungiyar Ecowas suka mayar da hankali a kai a jerin batutuwan da suka tattauna a wajen wannan taro karo na 42 da suke yi a Abuja. Suna wannan fafutukar ne da nufin ceto dimukurdiyya saboda kalubalen da ake fusknanta a yankin, inda matasa ke nuna jan ido ga shugabanin da suka zaba.

Karin bayani: ECOWAS: Taron ministocin tsaro a Abuja

Janar Christopher Musa ne ke shugabantar hafsoshin tsaron kasashen ecowasHoto: KOLA SULAIMON/AFP

Janar Christopher Musa da ke zama babban hafsan tsaron Najeriya kuma shugaban hafsohin tsaron kungiyar ta Ecowas ko CEDEAO ya ce: " Sarkakiyar da ke tattare da halin rashin tsaro da muke fuskanta ya nuna bukatar mu hada kai mu yi aiki tare ta fannin musayar bayanan sirri tare da aiki a kan iyakokinmu in har muna son samun nasarar wannan kalubale a yankinmu''

Akwai sauran matsaloli da kalubale da suka tabo kama daga batun watsuwar kanana makamai da ke fadawa hannun fararen hula da safarar miyagun kwayoyi. Amma barazanar da dimukurdiyya ke fuskanta a  kasashen Afrika ta Yamma shi ne ya fi daukar hankali, duk da cewa yana da alaka da watsuwar makaman.

Karin bayani:Kalubalen da ECOWAS ke fuskanta 

Dr Abdel-fatau  Musa da ke zama kwamishinan kula da harkokin siyasa tsaro da zaman lafiya na kungiyar Ecowas ya tabbatar da cewar: " Wannan taron karo na 42  dole ya fuskaaci jinkiri saboda halin siyasa da muka fuskaata a kasashenmu na Ecowas  ko Cedeao da suka hada da juyin mulki tare da  ficewar kasashen yankin Sahel daga Ecowas. Wannan na bukatar hada kai don daukar matakin da ya dace''.

Kwamishinan tsaro da zaman lafiya da siyasa n Ecowas Abdel-Fatau Musah (a Tsakiya)Hoto: Richard Eshun Nanaresh/AP Photo/picture alliance

Kokarin hada kai don a tafi tare ya ci gaba da zama muhimmin ginshiki a tsakanin jami'an tsaron kasashen yankin Afrika ta Yamma ciki har da  Kasar Ghana da ta samu hallartar taron. Kwararu irin su Dr Kabir Adamu, shugaban cibiyar Beacon da ke aiki a fannin tsaro a Najeriya da kasashen Sahel da kuma babban Hafsan tsaron Najeriya sun bayyana bukatar hada kai domin a gudu tare a tsira tare.

Karin bayaniECOWAS ta ce dakaru su kasance cikin shiri

Kasashen kungiyar ta Ecowas ko cedeao sun dade rabon da su fuskanci kalubale irin wannan da ke faruwa na rashin tsaro da guguwar juyin mulki da tirjiya daga matasa.