Sharhi: Kauce wa rikicin bayan zabe a Kamaru
October 28, 2025
Sakamakon zaben shugaban kasar kamaru na 2025 na da matukar rikitarwa, sobada ya yi hannun riga da duk wani abin da hankali zai iya dauka. Ya tabbatar da nasarar Paul Biya da ke zama shugaban mafi tsufa kuma mafi shafe yawan shekaru a kan kujerar mulki a duniya. Abin da ya fi daure kai shi ne, idan ban da zuwa Maroua da ya yi, bai yi yakin neman zabe ba, ballatana ma a san abubuwan da yake son yi wa 'yan Kamaru a cikin shekaru bakwai masu zuwa, amma aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe.
Mene ne hujja ko madogara?
Ita dai kasar Kamaru tana fuskantar matsin tattalin arziki a karkashin mulkin Biya na shekaru 42 ba tare da kakkautawa ba, lamarin da ya sa matasa kosawa da salon mulkin sa, saboda bai dace da zamani ba, baya ga gaza samar da ayyukan yi, da kuma rashin gano bakin zaren warware rikicin aware a yankin da ke magana da Ingilishi.
Karin Bayani: An shiga takun saka kan sakamakon zaben Kamaru
A daya hannun kuma, an shaidar da yadda matasan kasar Kamaru da ke da rinjaye a cikin al'umma suka tashi kwansu da kwarkwatansu wajen yin rajista, da kada kuri'a tare da kyautata wa dan takarara Issa Tchiroma Bakary fata domin su samu sauyin gwamnatin da suke bege. Saboda haka ne suka ki mayar da wukarsu cikin kube bayan bayyana sakamakon zaben da kotun tsarin mulki ta yi, inda suke ci gaba da zanga-zangar kin amincewa da sakamakon.
Sannan jam'iyyun adawa da kungiyoyi masu zaman kansu sun zaga sako da lungu na Kamaru domin fahimtar da al'umma alkiblar da suka dosa. Amma duk wadannan matakai suka je haka bata cimma ruwa ba, maimakon haka ma dai, aka samu abubuwan al'ajabi ko almara, inda wai sama da kashin 70% na al ummar yankin da ke magana da Ingilishi sun kada wa Biya kuria, a daidai lokacin da suke ci gaba da gwagwarmayar nemn ballewa daga kasar.
Rijiya ta bayar da ruwa guga ta hana?
Abin tambaya a nan shi ne: Wai shin rijiya ta bayar da ruwa amma guga ta hana ne? Tabbas sakamako da aka samu a mafi yawan rumfunan zabe bayan da aka kidaya kuri'a a ranar zabe sun sha bamban da na hukumar zabe ta Elecam da ma na kotun tsarin mulkin kasar Kamaru. Amma me wannan ke nufi? Yana nunawa cewar akwai lauje cikin nadi a tsarin zaben wannan kasa.
A hakikanin gaskiya, komai na iya faruwa tsakanin lokacin da aka yi kidaya kuri'u da lokacin da hukumar zabe ke tantance sakamakon domin mika wa kotu domin sanarwa. Wannan ne ma ya haifar da rashin yarda da tsarin zaben daga bangaren matasa da 'yan adawa, har ta kai jagoran adawa kin shigar da korafi a kotu domin a bi masa kadin nasarar da ya yi ikirarin samu. Irin wannan yanayi ba ya haifar da wani ci-gaba mai ma'ana a fannin zamantakewar al'umma.
Karin Bayani: An kama wasu jiga-jigan 'yan adawa a Kamaru
A fili yake cewar ba a taba gudanar da sahihin zabe a Kamaru ba tun bayan da kasar ta rungumi tsarin jamiyyun barkatai maimakon kafa tsarin dimukuradiyya. Dalili kuwa shi ne? Wayon a ci da Paul Biyaya girka na sa shi nada jami'an da ke masa biyayya ko kare muradunsa a dukkan matakai kama daga majalisa zuwa kotun tsarin mulki da hukumar zabe. Amma anya irin wannan salon cin zabe zai iya dawwama a Kamaru? Sam ba hanya mai dorewa ba ce.
Ina mafita?
Hanya mafi dacewa ita ce kwaskware tsarin zaben Kamaru daga kasa har sama, domin ya samu karbuwa ga kowa da kowa. Sannan gwamnati ta yi watsi da akidar kame da kisa ko tursasa 'yan adawa da masu zanga-zanga da ke kalubalantar zaben da ke cike da kura-kurai da tsananin son zuciya. Sannan talakawa su fara gani a kasa a fannin ababen more rayuwa da gudanar da shugabanci na gari, maimakon taron saba'una da tamanunu da casa'una da gwamnatin Biya ke kunsa.
A wannan karni na 25 da yanar gizo ya taimaka wa matasa tantance dan duma da kabewa, dole ne fadar mulki ta Yaoundé ta rika sara tana duban bakin gatari idan tana so ta guje wa rikicin bayan zabe da aka fuskanta a Côte d' Ivoire da Kenya a shekarun baya. Idan ba haka ba, komai na iya faruwa, abin da ya ci doma ba zai bar awai ba.