Turai za ta maye gurbin makamashin Rasha
March 8, 2022Hukumar gudanwar kungiyar Tarayyar Turai za ta gabatar da kudirin shirin gaggawa na kawo karshen dogara kan makamashin kasar Rasha. Yayin da yaki ci gaba da faruwa a Ukraine bayan kutsen da Rasha ta kaddamar, kasashen na Turai suna tunanin ban-kwana da makamashin Rasha cikin hanzari. Gas da ke zuwa kasashen Turai daga Rasha kan bi ta kasar Ukraine, kuma akwai tsoron saka takunkumi kan makamashin Rasha nan da lokaci kalilan.
Kashi 41 cikin 100 na makamashin Turai na fitowa daga Rasha.
Kana ana sa ran cikin wannan makon Shugaba Joe Biden na Amirka zai saka hannu kan ayar dokar tantance cinikayyan da kudin intanet da ake kira "Crypto" saboda dakile duk wata hanya da Rasha za ta bi wajen dauce wa tukunkumin karya tattalin arzikin da aka saka mata.