1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gangamin neman zaman lafiya a Najeriya

Uwais Abubakar Idris SB
May 7, 2021

Kokari na ganin makiyaya da sauran mutane sun rungumi zaman lafiya da kauce wa dora laifi da aka aikata kan wata kabila a matsayin matakin da zai iya taimaka shawo kan matsaloli na rashin tsaro a Najeriya.

Nigreria Fulani-Nomaden
Hoto: Luis Tato/AFP

Kungiyoyi sama da 150 ne dai  da rayinsu ya zo daya a kan wannan batu suka hadu domin wannan aiki saboda  ta'azara ta rashin tsaro a Najeiyar musamman garkuwa da jama'a da sauran aiyyuka na asha da ma ta'adanci ne dai ya dauki hankalin wadannan kungiyoyi da suka wo hobasa domin ba da tasu gudanawar a kokari na wanzar da zaman lafiya. Duk da cewa  kokari na cusa bukatar zaman lafiya a tsakanin alumma ne kan gaba sun yi kashedin cewa kafin cimma wannan matsaya fa sai an  daina dorawa wata kabila musamman ta Fulani laifi a matsayin ‘yan ta'ada. Alhaji Yusuf Musa Ardo shine shugaban kungiyar wanzar da zaman lafiya ta Walidirri ta Fulani a Najeriya.

Hoto: AFP/Luis Tato

Ta dai kai ga masu safara ta sayar da dabobi da sauran kayan abinci a Najeriyar daukan wannan ganagmi zuwa kasashen Kamaru da Chad inda suka tattauna a kan bukatar jawo hankalin abokanin sana'arsu musamman ma dai Fulani domin wanzar da zaman lafiya, bisa tunanen cewa amfani da wayar da kan jama'a yafi zama mai tasiri fiye da amfani da karfi. Comrade Mohammed Tahir shine shugaban kungiyar masu safarar dabbobi da kayan abinci ta Najeriya da ya hallarci wancan zama.

Karin Bayani:Najeriya: Matakin sulhu da 'yan bindiga

Munin wannan al'amari na rashin tsaro da a yanzu babu birni babu kauye ya sanya har ma da naso da take yi zuwa kasashen da ke makwabtaka da Najeriyar ya sanya  kungiyoyin farar hula da suka shiga wannan aiki ganin hanyar da aka dauka da suke ganin ba zata fa sqamarwa Najeriyar da makwabanta mafita mai kyawo ba.  Ambasada Badamasi Sadeeq Ibrahim shine shugaban kungiyar fara hula da ke wanzar da zaman lafiya da talafawa jama'a ta kasa da kasa.

A baya baya nan dai an ga tasirin shiga tsakani da sa baki da fitaccen malamin addinin Islama na Najeriya Sheikh Ahmed Gumi da hadin guiwar tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya fara samu. A karshe Alh Ysuf Musa Ardo na kungiyar Fulani masu wanzar da zaman lafiya  ya bayyana bukatarsu ga sauran alummu Najeriyar da ma na kasa da kasa.

Ana cike da fatan wannan yunkuri zai yi tasiri wajen taimaka kyautata wanazar da zaman lafiya tsakanin kabilun Najeriyar domin komawa a ci gaba da zama domin bunkasa kasa da ci gaban alumma.