Girka cibiyar samar da biza na Jamus a Kamaru
December 23, 2025
An kafa wannan cibiyar neman bizar zuwa Jamus a tsakiyar Yaoundé babban birnin kasar Kamaru, don magance hauhauwar neman izini da aka lura da ita a cikin 'yan shekarun baya-bayan nan. Christian Sedat, Jakadan tarayyar Jamus a Kamaru, ya bayyana cewa wannan cibiyar na da nufin saukake tsarin da ke da rikitarwa na neman biza, musamman ga dalibai, da masu neman gurbin horo, da ma'aikata da ke da kwarewa a fannonin kimiya da fasaha.
" Za mu iya sarrafa karin takardun neman biza har guda 500 a kowane wata, sakamakon hadin gwiwarmu da VFS Global. Wannan zai ba mu damar fitar da ayyukan neman izini zuwa wata cibiya a manyan fannoni kamar karatu da neman ilimi da kwarewa a fannin aiki."
Cibiyar neman bizar na aiki ne da fasahar zamani, musamman ma wajen daukar sawun yatsan hannu na biometric, kuma tana tallafa wa wadanda ke neman izinin zuwa Jamus domin hadewa da iyalansu, da wanda za su yi karatu, da wadanda za su je aiki.
Christiane Tatsinkou, shugabar wata cibiyar koyar da harshen Jamusanci na ganin cewar wannan cibiyar za ta taimaka sosai wajen saukake tsarin neman biza.
"Daliban da ke zuwa nan don koyon Jamusanci da nufin Jamus sun kai kashi 90% na wadanda suke nan."
Karkashin wannan shiri, karin matasa Kamaru za su iya tsara makomar a Jamus. Wannan ne abin da ke faruwa ga Stéphanie, mai shekaru 23, wacce ke karatun Jamusanci tun tssawon watanni takwas don neman koyon aikin jinya a Jamus. matashiyar tana daukar kasar a matsayin daya daga cikin kasashe mafi dacewa a fannin samun horo.
"Na dade ina mafarkin zama likita. An gaya mini cewa Jamus, kasaitacciyar kasa ta yin karatun likitanci, don haka na yanke shawarar gwada ta."
Wasu 'yan Kamaru sun riga suka samu biza a wannan cibiya, kamar Adrien, mai shekaru 24, wanda ya tafi samun hora a fannin jinya.
" Ga wanda ya san abin da yake so na rayuwa mafi kyau a Jamus, zai iya nasarar sajewa tare da gina kansa."
Da wannan sabon ofishin, Jamus na fatan saukake hanyoyin samun biza daga Kamaru, lamarin da zai rage yawan lokaci wajen zuwa Jamus ta hanyar da ta dace.