1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

APC tana neman kawo karshen rikicin da jam'iyyar ke fuskanta

Suleiman Babayo
November 3, 2021

A Najeriya rigingimun jam'iyyar APC mai mulkin kasar na ci gaba da zama babban kalubalen yayin da take fuskantar babban taro, abin da ya kai ga kafa kwamitin sulhun da ya gudanar da wani taro a Abuja.

Nigeria, Abuja: Präsident Muhammadu Buhari begrüßt seine Unterstützer
Hoto: Reuters/B. Omoboriowo

Da yawa cikin ‘yayan jamiyyar ta APC mai mulki sun dugunzuma tare da fusata, fushin da ya sanya mika ragamar jamiyyar a hannun  kwamitin riko a jam'iyyar karkashin gwamnan jihar Yobe Mai Malla Buni domin gyara lamura, dama kafa kwamitin sulhunta 'yan jam'iyyar ta APC mai mulki a Najeriya. Irin yadda rigingimun suka sake daukan sabon salo a jihohi da dama da aka samu bangarori biyu ya nuna halin na rikicin jamiyyar. Alhaji Ahmadu Haruna Zago na cikin wadanda suka fusata a jam'iyyar ta APC duk da matakin da jam'iyyar ya dauka.

Karin Bayani: Najeriya: Zaben shugabannin manyan jam'iyyun siyasa a jihohi ya bar baya da kura

Hoto: DW/U.Musa

Tun bayan awon gaba da tsohon shugaban jam'iyyar Adams Oshimohole har yanzu da sauaran ‘yan jam'iyyar da ke jan daga a kan korafin da suke da shi, domin duk da mataki na haramta kai lamarin gaban kotu sun tirje sun ma ki janyewa. Sanata Abdullahi Adamu shine shugaban kwamitin sulhunta ‘yayan jamiyyar da suka gudanar da taro a kan aikin da ke gabansu a Abuja.

Rikici ko takadama akan ce gishiri ne ga dimukurdiyya musamman a tsari na cikin gida iri na jam''iyyu, da akan samu ra'ayoyi mabambanta.

A yanzu dai jam'iyyar APC na hali na kalon ganin iyakar gudunka da babbar jamiyyar adawa ta PDP ke ,mata wacce ta kammala babban taron na kasa tare da zaben sabbin shugabani a yanayi na cimma sulhu ga mafi yawan mukaman da aka zaba.