Sauran mutane sama da 40 da gini ya danne a Afirka ta Kudu
May 8, 2024Jami'an agaji a kasar Afirka ta Kudu na ci gaba da aikin ceto mutane sama da 40 da har yanzu ke karkashin baraguzan gini mai hawa 5 da ya rufta musu, a daidai lokacin da suke tsaka da aikin gina shi, inda ya zuwa yanzu suka samu nasarar kubutar da mutane 26.
Karin bayani:Tsohon shugaban Afirka ta Kudu ya tsallake rijiya da baya
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai ginin ya ruguje a yankin George da ke kusa da birnin Cape Town, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6, daga cikin ma'aikata 75 da ke tsaka da aiki a lokacin faruwar lamarin.
Karin bayani:WHO ta ce babu sauran gurbataccen maganin tari a Afirka
Jami'an agajin dai sun samu damar magana da mutane 11 da ke karkashin ginin, kuma suna amfani da karnuka masu sansano abubuwa, sannan akwai ma'aikatan lafiya jibge a wurin, don samar da duk wani taimakon gaggawa da ake bukata yayin aikin ceton.