1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Da sauran aiki gaba bayan taron Minsk

Suleiman BabayoFebruary 12, 2015

Bayan kwashe lokaci mai tsawo ana tattauanawa a birnin Minsk na kasar Belarus, an amince da shirin tsagaita wuta a yankin gabashin kasar Ukraine.

Ukraine Krise Gipfelteilnehmer in Minsk
Hoto: Reuters/Grigory Dukor

A wannan Alhamis an samu jinkirin sa'o'i biyu kafin komawa zauren taron neman kawo karshen rikicin da ake samu a gabashin kasar Ukraine tsakanin gwamnati da 'yan aware masu goyon bayan Rasha. Shugaba Francois Hollande na Faransa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun kwashe tsawon daren Laraba suna tattauna shirin na tsagaita wuta.

A wani tsakaitaccen jawabi Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bayyana cewa an amince da fara aiki da shirin tsagaita wuta daga ranar 15 ga wannan wata na Fabrairu.

"Abin da ya sa aka dauki tsawon lokaci kafin amince wa da shirin tsagaita wuta, ina tsammani saboda mahukuntan birnin Kiev ba su amince da tattaunawa kai tsaye da wakilan al'umar Donetsk da Luhansk ba. Duk da cewa ba su amince da su ba, ya dace mu fuskanci zahirin abin da ke faruwa."

Hoto: picture-alliance/AP Photo/ S. Grits

Shugaba Putin ya kara da cewa muddin ana bukatar samun sulhu mai dorewa, dole a yi tattaunawa ta kai tsaye da duk bangarorin sannan ya tabbatar da cewa shirin tsagaita wutar zai fara aiki daga daren ranar 15 ga wannan wata na Fabrairu.

Tababa ga kokarin warware rikicin Ukraine

Tuni wasu daga cikin mahalarta taron kamar ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier suka nunar da cewa duk da ci-gaba babu tabbaci na cewa an samu maslaha.

Shugaban Francois Hollande na kasar Faransa ya nunar da karfin gwiwa na fara amfani da shirin tsagaita wutar.

"Mun kwashe tsawon dare kuma ya dauki tsawon lokaci, amma mun cimma yarjejeniya. Yarjejeniya ta tsagaita wuta da kuma sasantawa ta fannin siyasa baki daya. Wannan tsagaita wuta za ta fata aiki ranar 15 ga watan nan na Fabrairu. Kuma abin da ya shafi siyasa zai biyo baya."

Petro PoroschenkoHoto: AFP/Getty Images/S. Gapon

Tuni 'yan siyasa daga kasashen Turai suka fara yaba wa matakin sasanta rikicin na gabashin Ukraine.

Yabo ga yunkurin samun maslaha a Ukraine

Stefan Liebich mai kula da harkokin waje na jam'iyya mai ra'ayin sauyi ta Jamus ya jinjina wa shugabannin kasashen.

"Ina matukar jinjina wa shirin da shugabar gwamnati da shugaban Faransa suka dauka, ganin yadda a lokacin baya-bayan nan an samu mutuwar mutane da yawa. Dubban daruruwan mutane sun zama 'yan gudun hijira, saboda rashin daukan mataki na siyasa daga mahukuntan Mosko, da birnin Kiev, da Lugansk da kuma Donezk."

Yayin da ake kan hanyar warware rikicin kakakin sojin Ukraine ya bayyana cewa an shigar da manyan makamai gabashin kasar daga kasar Rasha.