SiyasaYuganda
Zaben Yuganda: Har yanzu da sauran tsalle
January 20, 2026
Talla
Mai shekaru 51 a duniyar Janar Muhoozi Kainerugaba da ke fatan ya gaji mahaifinsa wanda ke mulkin mutu ka raba a Yugandan, ya wallafa a shafinsa na X cewa sun halaka 'yan ta'addan jam'iyar adawa ta NUP 22, kuma yana fatan na 23 ya zama Kabobi. Kabobi dai lakabi ne da ake wa jagoran adawar kasar Bobi Wine da ya shiga buya tun bayan da ya fadi zaben da aka gudanar a makon da ya gabata dai, ya bayyana zaben da aka sake yi wa Shugaba Museveni mai shekaru 81 a duniya a karo na bakwai da na je ka na yi ka.