Har yanzu tana kasa tana dabo a Pakistan
July 10, 2007Jami´an tsaron Pakistan sun kutsa kai cikin harabar wani fitaccen masallaci dake Islamabad, inda masu tsattsauran ra´ayi na Islama suka mamaye tsawon mako guda. Daukar wannan matakin dai, ya biyo bayan kokarin da jami´an tsaron keyi ne na kubutar da mutanen da ake garkuwa dasu. Jami´an tsaron sun yanke daukar matakin ne bayan da aka gaza cimma sultu, a tsakanin bangarorin biyu .An dai kiyasta cewa daliban masu tsattsauran ra´ayi na garkuwa da mutane kusan dari uku, da yawa yawan su mata da kuma kana nan yara a cikin masallacin. A kalla ya zuwa yanzu mutane 43 ne suka rasu, cikin su kuwa har da soji uku. Mai magana da yawun gwamnatin kasar ya tabbatar da cewa har yanzu, jami´an tsaron na ci gaba da farautar tsagerun, a dai dai lokacin da ake ci gaba da musayar wuta a harabar masallacin a tsakanin bangarorin biyu.