1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Har yanzu tsugune ba ta ƙare ba a Libiya

October 18, 2012

An samu wani sabon rikicin da ya kai ga salwantar rayukan mutane 11 a garin Bani Walid na ƙasar Libiya.

Hoto: Getty Images

Aƙalla mutane 11 sun hallaka yayin da wasu fiye da 70 su ka samu raunika, lokacin da tsaffin 'yan tawaye masu alaƙa da gwamnatin Libiya, su ka kai hari kan garin Bani Walid, da ake ɗauka tungar magoya bayan hamɓararren shugaba marigayi Mu'ammar Gaddafi.

Mataimakin shugaban wani asibitin birnin, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, an kai gawauwakin mutane bakwai asibitin ciki harda wata 'yar shekaru 14 da haihuwa. Sannan wani shaidan gani da ido ya bayyana ganin gawauwaki huɗu.

Wannan sabon tashin hankali na ranar Laraba, ya tabbatar da cewa, har yanzu ƙasar ta Libiya ba ta gama warwarewa daga rikicin da ya kai ga kifar da gwamnatin marigayi Gaddafi ba, ko da ya ke an gudanar da zaɓe tare da girka majalisar dokoki.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal