1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Har yanzu tsugune-tashi ba ta kare ba a Sudan

Gazali Abdou Tasawa MAB
April 13, 2019

Masu zanga-zanga neman sauyi a Sudan sun ci gaba da zaman dirshen a gaban hedikwatar sojojin kasar duk da murabus da Ahmed Awad Ibn Auf ya yi tare da sanar da Abdel Fattah al-Burham Abdelrahmane a matsayin sabon shugaba.

Sudan Proteste in Khartum
Hoto: Reuters

Masu zanga-zanga neman sauyi a Sudan sun ci gaba da zaman dirshen a wannan Asabar a gaban hedikwatar sojojin kasar da ke a birnin Khartoum duk da murabus din da shugaban hukumar mulkin soja ta rikon kwaryar kasar Ahmed Awad Ibn Auf  da maye gurbinsa da Abdel Fattah al-Burham Abdelrahmane babban speto na rundunar sojin kasar 

Masu zanga-zangar sun ce suna jira sabbin umurni daga jagororinsu kan ko su ci gaba da zaman dirshen din ko kuma su dakatar da shi. Wannan mutun na daga cikin masu ci gaba da zaman dirshen din a wannan Asabar:.

"Ya ce " lalle juyin juya halinmu ya gama da Ibn Auf da Al-Bashir. Abdulfatah al-Burhan ya dauka a yanzu. To amma wanene shi? minene banbancinshi da sauran. To ko shi ba za mu yi masa saussauci ba. muna jiran jawabinsa na farko don sanin manufarsa kafin yanke hukuncin abin da ya dace mu yi"

Shi ma dai shugaban hukumar leken asirin kasar ta Sudan Salah Gosh wanda ya jagoranci matakin murkushe masu zanga-zangar a watannin baya bayan nan ya yi murabus daga mukaminsa a wannan Asabar kuma tuni sabon shugaban rikon kwarya ya amince da murabus din nasa.

A safiyar wannan Asabar dai sojojin sun janye shingaya da mutane suka gitta kan hanyar zuwa hedikwatar tasu, har ta kai ana hira cikin raha tsakanin sojojin da masu zanga-zangar wadanda a yanzu suka shiga aikin share filin a yayin da a dabra daya wasunsu ke dafa abinci da shayi a gaban hediwatar sojojin kasar inda suka share kwanaki bakwai suna zaman dirshen.